Home Back

Kwana 1 da Hukuncin Kotu, Gwamna Ododo Ya Dauki Mataki Kan Ciyamomi 21

legit.ng 2024/10/5
  • Gwamnatin jihar Kogi ta kara wa'adin shugabannin riko na kananan hukumomi 21 da ke jihar da suke shirin sauka
  • Majalisar jihar ita ta amince da tsawaita wa'adin bayan Gwamna Usman Ododo ya rubuta mata takarda kan lamarin
  • Wannan na zuwa ne yayin da shugabannin rikon ke karkare wa'adinsu a ranar 8 ga watan Yulin 2024 kafin karin wa'adin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Majalisar jihar ta kara wa'adin shugabannin rikon ne zuwa watanni shida domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Wannan mataki na zuwa ne yayin zaman Majalisar a yau Juma'a 5 ga watan Yulin 2024 a birnin Lokoja, cewar Channels TV.

Gwamna Ododo shi ya tura wasikar neman karin wa'adin ga shugabannin riko na kananan hukumomin ga Majalisar.

Ododo a cikin takardar ya bayyana matsalar kudi daga cikin dalilan da zai hana gudanar da zaben kananan hukumomin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin Majalisar, Hon. Umar Yusuf shi ya karanto takardar ga mambobin inda ya hori shugabannin rikon kan aiki.

Hon. Umar ya bukace su da su zama jakadun kananan hukumomin da suke jagoranta a kowane lokaci.

Wa'adin shugabannin rikon kananan hukumomi 21 zai kare ne a ranar 8 ga watan Yulin 2024 ta wannan shekara.

Bayan matakin Majalisar na karin wa'adin, shugabannin za su kammala wa'adin nasu a ranar 8 ga watan Janairun 2025.

Kotu ta yi hukunci kan zaben Kogi

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben jihar Kogi da aka gudanar.

Kotu ta yi fatali da korafin dan takarar jam'iyyar SDP, Murtla Ajaka da ke kalubalantar zaben Usman Ododo na APC.

Wannan na zuwa ne bayan sanar da Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar na watan Nuwambar 2023.

Asali: Legit.ng

People are also reading