Home Back

Mahukuntan Saudiyya sun kare mace mace saboda tsananin zafi

dw.com 2024/7/3
Hoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/picture alliance

Ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar, masarautar ta yi iyakar kokarinta, amma akwai kuskure a bangaren mutanen da ba su yi la'akari da hadarin da ke tattare da yanayin ba, a martanin farko da ke fitowa daga bangare gwamnati kan mace-macen.

Kididdigar da AFP ya gabatar a wannan Juma'a, wanda ya hada bayanan hukuma da rahotanni daga jami'an diflomasiyya da ke da hannu a martanin, ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai 1,126, fiye da rabinsu daga kasar Masar.

Gwamnatin Saudiyya ta tabbatar da mutuwar mutane 577 a cikin kwanaki biyun farko masu tsanani na aikin hajji: Ranar Asabar lokacin da mahajjata suka taru na tsawon sa'o'i na addu'o'i a cikin rana mai zafi a dutsen Arafat, da kuma Lahadi, a lokacin da suka yi "jifan shaidan" na farko a Mina.

A baya dai mahukuntan Saudiyya sun ce mahajjata miliyan 1.8 ne suka halarta a bana, kamar na bara, kuma miliyan 1.6 sun fito ne daga kasashen waje.

People are also reading