Home Back

Majalisar Dokokin Kano za ta ƙirƙiri Sarakuna masu daraja ta biyu a Kano

premiumtimesng.com 2024/9/28
SUNAYE: Ƴan majalisar dokokin Kano 9 sun canja sheka zuwa jam’iyya mai alamar kayan marmari NNPP

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Kano, Honorabul Lawal Hussaini ya bayyana cewa za a ƙirƙiri Sarakuna masu daraja ta biyu a Jihar Kano.

Gidan Radiyon Freedom da ke Kano ya ruwaito cewa: *Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Kano Lawan Hussaini Chediyar ‘Yangurasa ya shaida wa Freedom Radio cewa za a ƙirƙiri ƙarin masarautu masu daraja ta biyu a Kano.

Ya ce gobe Juma’a ne zai gabatar da ƙudirin a Majalisar Dokokin Kano.

Shi ne dai Ɗan Majalisa wanda ya gabatar da ƙudirin soke dokar da gwamnatin Ganduje ta yi, wadda ta ƙirƙiro sabbin masarautu, wadda aka rushe a yau Alhamis.

Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan bayyana sake naɗa Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano baki ɗaya, bayan rushe sarakuna biyar da Ganduje ya ƙirƙira.

People are also reading