Home Back

Sojojin Najeriya Sun Dira Sansanin Manyan Ƴan Bindiga 3 a Arewa, Sun Kashe da Yawa Ranar Sallah

legit.ng 2024/5/20

Jihar Zamfara - Rinɗunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta samu nasarar halaka ƴan bindiga masu ɗumbin yawa a yankunan kananan hukumomin jihar Zanfara ranar Sallah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ruwan wutar NAF ya yi ajalin ƴan bindiga masu yawa a sansanin kasurgumin ɗan bindigan nan, Abdullahi Nasanda, a ƙaramar hukumar Zurmi.

Haka nan kuma ƙarin luguden sojin ya kashe da yawa daga cikin ƴan bindiga a sasanin hatsabibin ɗan bindiga, Mallam Tukur a ƙaramar hukumar Gusau jiya Laraba.

Kakakin rundunar, Air Vice Marshall Edward Gabkwet, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da NAF ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu.

Ya ce sojoji sun kai faramkin ta sama ne bayan tabbatar da bayanan sirri da aikin leken asiri.

"Bayan sun tabbatar da cewa ayyukan na su ya yi daidai da na ‘yan ta’adda, jiragen sojoji sun bi ta sama sun saki wuta , wanda ya yi sanadin kashe ƴan bindiga da dama.
"Haka nan an gudananr da aikin ISR a sansanin Mallam Tukur, nan ma aka gano ƴan bindigar, ruwan wuta ta sama ya halaka su da yawa kuma an ga rumfunan su duk sun ƙone"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sojojin ba su tsaya nan ba sun kuma kai samame kauyen Kani Kawa a karamar hukumar Maradun, inda suka gano mafarakar ƴan bindiga da ƙayan aikinsu, suka murƙushe su."

- Air Vice Marshall Edward Gabkwet.

Asali: Legit.ng

People are also reading