Home Back

Masu tsattsauran ra'ayin riƙau sun kama hanyar nasara a zaɓen Faransa

bbc.com 3 days ago
Magoya bayan jamiyyar RN

Asalin hoton, Getty Images

Dubban Faransawa sun cika titunan birnin Paris, domin zanga-zangar kin jinin jam'iyyar National Rally, ta masu tsattsauran ra'ayin rikau, kwana daya bayan zaben 'yan majalisu, da sakamakon farko ke nuna jam'iyyar na sahun gaba.

Daman Firaminista Gabriel Attal mai sassaucin ra'ayi ya yi gargadi kan jam'iyyar, ta yi kane-kane a kan mulki, tare da Faransawa su tabbatar ba su kada musu kuri'a daya ba a zagayen zaben na biyu a ranar Lahadi mai zuwa.

Da wannan sakamako na zaben na zagayen farko na majalisar dokokin yanzu jamiyyar masu tsattsauran ra’ayin rikau ta National rally, ta kama hanyar nasarar mulki.

Magoya bayan jamiyyar ta Marine Le Pen mai kyamar baki na cike da murna inda jagorar tasu ke cewa an share hadakar Macron, sai buzunsu.

Jamiyyar ta samu kashi 34 cikin dari na kuri’u, inda hadakar masu ra’ayin kawo sauyi ke bin baya da kashi 28.1 cikin dari yayin da gamayyar su Shugaba Macron ta kasance da kashi 22 cikin dari na kuri’un.

Sai dai yayin da ake gangamin nuna kyama ga nasarar tasu, da neman taka musu birki na kama mulki, jagoran jamiyyar ta RN, Jordan Bardella, mai shekara 28, ya ce zai kasance Firaminista ne ga dukkanin al’ummar Faransa idan suka ba su kuri’arsu.

Idan har wannan hamayya ba ta yi nasara ba, jam’iyyar ta yi galaba har ta samu rinjayen kuri’u da suka fi yawa da ake bukata, to a dole Shugaba Macron zai yi aiki kenan da jam’iyyar ta masu tsattsauran ra’ayin rikau din kenan a ragowar shekaru uku na na mulkinsa.

Kuma daman wannan abu ne da hatta ‘yan gamayyarsa suka hanga da cewa ya yi kasassaba, da ya kira zaben na wuri.

Tuni ma har Firaminista Gabriel Attal ya fara bayar da kai, yana cewa jamiyyar ta National Rally, na dab da kama mulki, ganin yadda ta yi nasara a zagen farko na zaben.

Sai dai duk da haka Firaministan ya bukaci masu zabe da kada su bai wa jamiyyar ko da kuria daya kuma a zagaye na biyu na zaben na Lahadi mai zuwa.

Christopher Weissberg, na gamayyar su Macron, ya jaddada kuren da suke ganin Shugaba Macron din ya yi mako uku da ya gabata kan neman a yi zaben na wuri da ya yi :

Ya ce, ''ya yi kokarin fayyace matsayin jamiyyu daban-daban, to amma ta hanyar da za ta kasance mai wuya a samu rinjayen nasarar da za ta bayar da cikakkiyar dama ga masu tsattsauran ra’ayin rikau. Muna bukatar mu yi hadakar da za ta hana ganin takaicin masu tsatsauran ‘arayin rikau kama mulki a karon farko a Faranbsa tun bayan yakin duniya na biyu.''

Shi ma Shugaba Macron na na rokon da a samu hadakar da za ta hana jam'iyyar ta National Rally cimma burinta na kafa gwamnati.

People are also reading