Home Back

Zaben majalisar dokokin Turai na 2024

dw.com 2024/7/3
Majalisar dokokin Turai a Straßburg
Majalisar dokokin Turai a Straßburg

Zaben da za a yi cikin kasashe 27 mambobin kungiyar Tarayyar Turai, an shafe watanni ana yakin neman zaben wanda ake yi duk bayan shekaru biyar, domin samar da 'yan majalisa sama da 700 da suke da kujeru a majalisar dokokin. Wannan kuma ke zama gagarumin zabe na biyu a duniya da ya kunshi mutane masu yawa kimanin milyan 350 bayan zaben kasar Indiya.

Roberta Metsola shugabar majalisar dokokin Tarayyar Turai ta bukaci masu kada kuri'a bisa sauke nauyin da ke kansu ranar zabe:

"Kuna ganin wannan kujerun majalisar dokokin fiye da 700 da ke gaban ku. Ko kun kada kuri'a ko ba ku kada ba, za a cike gurbinsu. Yanzu kuna da zabi ko dai ku kasance wadanda za su tantance wadanda za su zauna kan kujerun kuma ku kasance wadanda ba sa cikin wadanda aka dama da su."

A kasashen Turai irin Jamus, batutuwan tsaro da yakin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine suka mamaye yakin neman zaben. Batun bakin haure bai taka rawar a zo a gani ba.

Akwai 'yan siyasa da suke ganin Shugaba Vladimir Putin na Rasha da China karkashin Shugaba Xi Jinping a matsayin abin koyi ga kasashen na Turai, sai dai tuni jiga-jigan 'yan siyasa suka yi watsi da irin wannan tunanin, inda Olaf Scholz shugaban gwamnatin Jamus ya jaddada tasirin kungiyar Tarayyar Turan:

"Gare mu Turai tana da matukar muhimmancin da za mu zura ido a lalata ta ba. Akwai masu kishin kasa a Jamus da suke neman ficewa daga Tarayyar Turai. Sannan wasu suna ganin Rasha karkashin Shugaba Putin da China karkashin Shugaba Xi Jinping a matsayin abin koyi ga Turai. Kana akwai masu neman ganin an wargaza kungiyar Tarayyar Turai. Sai dai hadewa na kasashen Turai ke samar da tsaro da makoma mai inganci a gare mu."

Ursula von der Leyen shugaban hukumar gudanarwar Tarayyar Turai ta yaba musamman ga 'yan siyasa irin Firaminista Giorgia Meloni ta kasar Italiya wadda take da ra'ayin mazan jiya kuma take nuna sanin ya kamata da goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai:

"Abin da muke nunawa shi ne ko masu goyon bayan kungiyar kasashen Turai irinsu Meloni ta Italiya tana adawa da abin da Shugaba Putin na Rasha ke yi, kuma ta fito fili game da haka, da goyon bayan mutunta dokoki. Idan haka ya ci gaba da za mu yi aiki tare."

A kasashen Faransa, da Italiya, da Netherlands, da Belgium, da Austriya gami da Hungari masu matsanancin ra'ayoin mazan jiya suna kara tasiri tsakanin masu zabe.

People are also reading