Home Back

APC ta dakatar da Dakta Abdullahi Ganduje daga jam’iyyar

dalafmkano.com 2024/5/17

Jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.

Mai bai wa jam’iyyar shawara a ɓangaren shari’a a mazaɓar Ganduje, da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Halliru Gwanzo, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai a jihar ta Kano, kamar yadda jaridar online ta Nigerian Triker ta rawaito.

Halliru Gwanzo, ya kuma ce sun ɗauki matakin dakatar da tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin jihar Kano take masa a kan yin badaƙala da kuɗin al’ummar jahar.

People are also reading