Home Back

Jirgin Sama Dauke da Manyan Mutane Daga Abuja Ya Ci Karo da Cikas a Legas, an Gano Dalili

legit.ng 2024/5/19

Mutane da dama sun shiga fargaba yayin da wani jirgin sama ya kauce hanya a jihar Legas da ke Kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - An shiga fargaba yayin da jirgin sama ya kauce hanya a jihar Legas bayan kwaso fasinjoji daga Abuja.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata 23 ga watan Afrilu a jihar yayin da jirgin ya yi saukar gaggawa tare da kauce hanya.

Channels TV ta tattaro cewa lamarin ya rutsa ne da jirgin saman kamfanin 'Dana Air' wanda ya taho daga Abuja.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu karin bayani ba, sai dai an tabbatar da cewa babu rasa rai.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne saboda dalilin ruwan sama da aka tafka da safiyar yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin saman an tabbatar ya na dauke da fasinjoji akalla 83 daga birnin Abuja zuwa Legas.

Karin bayanai na nan tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading