Home Back

Yayin da CBN Ke Kokarin Kawo Gyara, Naira Ta Samu Matsala a Karo Na 2, Dala Ta Tashi

legit.ng 2024/5/20
  • Kwanaki kadan bayan sanar da faduwar darajar naira, a jiya Litinin 22 ga watan Afrilu ta sake cin karo da matsala
  • Naira ta sake faduwa akalla da kaso 5.5% idan aka kwatanta da ranar Juma'a 19 fa watan Afrilun wannan shekara
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnan bankin CBN, Yemi Cardoso ya yi alkawarin inganta darajar naira domin samun daidaito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - A karo na biyu cikin kwanaki, naira ta sake faduwa a kasuwanni yayin da dala ta tashi.

Darajar naira ta fadi da kaso 5.5% idan aka kwatanta da farashin N1,169 kan dala a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu.

TheCable ta tattaro cewa a yanzu ana siyar da dala kan farashin N1,234 a kasuwanni idan aka kwatanta da kwanakin baya.

Hakan ya biyo bayan sake faduwar naira a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu da kaso 1.3% a kasuwanni.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso ya ce suna bakin kokarinsu dokin inganta naira a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cardoso ya bayyana haka ne a ranar Asabar 20 ga watan Afrilu kwana daya bayan naira ta sake faduwa.

Gwamnan ya ce bankin ya na aiki tukuru domin tabbatar da farashin naira ya inganta yadda ya kamata.

Karin bayani na nan tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading