Home Back

Gaza: Amurka ta gabatar da sabon shirin tsagaita wuta

dw.com 2024/6/26
Hoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

Biden ya ce da farko sabuwar tattaunawar na bukatar tsagaita wuta na makonni shida, inda Isra'ila za ta janye sojojinta daga yankunan da ke da mutane a Zirin Gaza. Ya ce hakan zai bayar da dama ga Falasdinawan da suka rasa muhallansu su koma gida yayin da ita kuma kungiyar Hamas ana bukatar ta saki mutanen Isra'ila da take rike da su domin bude kofar sakin Falasdinawan da ke tsare a gidan kason Isra'ila.

Kungiyar Hamas ta ce wannan yunkuri ne mai kyau kuma akwai alamun nasara, yayin da Isra'ila ta ce duk da wannan kokari akwai bukatar ta kakkabe kungiyar Hamas daga doron kasa. Amma MDD da kasashen kungiyar Tarayyar Turai ciki har da Jamus sun nuna amincewarsu ga sabuwar tattaunawar sulhun da ake sa ran zango na biyunta zai samar da tsagaita wuta ta din-din a yankin na Zirin Gaza.

People are also reading