Home Back

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta tabbatar da labarin PREMIUM TIMES kan barazanar ISWAP

premiumtimesng.com 2024/8/22
Ana batakashi tsakanin ‘yan ta’adda da Sojojin Najeriya a Madallah Abuja

Hedikwatar Tsaro ta Rundunar Sojojin Najeriya (DHQ), ta bayyana cewa tabankaɗo wani mummunan shiri da Boko Haram ɓangaren ISWAP ke yi na ƙoƙarin afka wa Najeriya da munanan hare-haren ƙunar-baƙin-wake, a kan wasu sassa daban-daban na ƙasar nan.

Wannan bayani wanda ya fito daga Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar da wani rahoton musamman da PREMIUM TIMES ta buga a ranar Laraba.

Buba ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Alhamis, inda yake gaggawar fargar da mutane yiwuwar kai hare-haren na ƙunar-baƙin-wake da ‘yan ta’adda zasu kai.

“Kamar yadda aka sani, mun ɗauki ƙwararan matakan hana afkuwar hare-haren, saboda wasu a baya an sha yin irin haka, amma muna samun nasarar daƙile shi.”

Kwana ɗaya kafin Rundunar Sojojin Najeriya su yi wannan gargaɗin, wannan jarida ta buga labarin mai ɗauke da cewa ISWAP na shirin kai hare-haren ta’addancin ƙunar-baƙin-wake a wasu wurare a cikin ƙasar nan, musamman gidajen kurkuku da wuraren da ake hada-hadar fetur da gas.

A ranar Laraba dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa, “Barazanar afka wa Najeriya da hare-haren ƙunar-baƙin-wake daga ISWAP ta sa jami’an tsaro shirin ko-ta-kwana”.

A labarin, an bayyana cewa alamomi na nuna tabbacin cewa jami’an tsaro da jami’an leƙen asiri na zama cikin shirin ko-ta-kwana, biyo bayan wata barazanar afka wa wasu wurare da hare-haren ƙunar-baƙin-wake da Boko Haram ɓangaren ISWAP suka yi.

Wannan lamari ya zo kwanaki 12 bayan wani harin ƙunar-baƙin-wake da aka kai a yankin Gwoza, cikin Jihar Barno, wanda ya halaka mutum 20 a ranar 29 ga Yuni. Kuma ISWAP ɗin ne suka kai harin ta hanyar amfani da mata ‘yan ƙunar-baƙin-wake.

Har zuwa yanzu dai ba a sanar wa jama’a su yi kaffa-kaffa ba, amma dai PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa gwamnati ta umarci dukkan ɓangarorin tsaro su yi shirin ko-ta-kwana.

PREMIUM TIMES ta ji cewa jami’an tsaro sun yi amanna ISWAP na shirin kai munanan hare-hare a gidajen kurkuku da kuma wasu wurare na harkokin fetur da gas.

A ranar Laraba ɗin nan ce PREMIUM TIMES ta samu wani bayanin sirri na jami’an leƙen asiri a ranar 10 ga Yuli cewa jami’an tsaro su yi shirin yiwuwar ISWAP za su kai munanan hare-haren ƙunar-baƙin-wake.

Wuraren da aka bayyana Boko Haram ɗin na shirin kai hari sun haɗa da Gidan Kurkukun Kuje, Abuja, Gidan Kurkukun Kaduna, na Fatakwal da na Kirikiri a Legas, da ma wasu wuraren daban-daban.

Haka kuma su na shirin afka wa bututun mai wanda ake kan aikin sa daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, mai tsawon kilomita 614, wanda kamfanin NNPC ke kan yi.

Ɓangarorin tsaron ƙasar nan biyu da PREMIUM TIMES ta tuntuɓa a ranar Laraba, ba su tabbatar da barazanar ISWAP ɗin ba, amma dai sun tabbatar cewa su na cikin shirin ko-ta-kwanan daƙile duk wata barazana.

Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku, Umar Abubakar, ya ce hukumar sa ba za ta ɗauki wannan barazana a matsayin abin wasu ko cika-bakin ISWAP ba.

“Kuma kada ka manta, muna aiki tare da ‘yan sanda da sojoji. Ba za mu yi wasa da irin wannan bayani ba.” Inji shi.

Ta’addancin ISWAP A Najeriya:

A ranar Lahadi PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton da ISWAP ta ce, ”Mun kai hare-hare 232 a Najeriya, farmaki 1,115 a Afrika ta Yamma a cikin watanni ukun farkon 2024”.

Cikin wani rahoton baya-bayan nan da ƙungiyoyin ta’addanci biyu suka fitar na haɗin-gwiwa, ISWAP da ISGS sun bayyana cewa sun kai hare-haren ta’addanci sau 232 a Najeriya, a cikin watanni ukun farkon 2024, wato Janairu, Fabrairu da Maris.

Sun bayyana cewa a waɗannan hare-hare sun kashe mutum 609 a Najeriya, yayin da a Afrika ya Yamma baki ɗaya kuwa sun kai hare-hare 1,115.

ISWAP ƙungiyar Boko Haram ce wadda ta ɓalle daga biyayya ga Shekau a cikin 2016, ta riƙa kiran kan ta IS, wato Islamic State, Reshen Afrika ta Yamma.

Ƙungiyar ta Boko Haram ta yi kaka-gida ne a yankin Tafkin Chadi, ta mamayi cikin Najeriya, Kamaru da Nijar da Chadi.

Cikin wani jadawalin farfaganda da ISWAP suka fitar a ranar 1 ga Yuli, sun ce ISWAP sun kai hare-hare sau 536 wanda ya yi sanadiyyar kisan mutum 2,142.

PREMIUM TIMES ta yi nazarin jadawalin wanda ya nuna cewa ISWAP da ISGS sun kai hare-haren ta’addanci sau 1,115 a Afrika ta Yamma.

Wannan adadin ya nuna hare-hare da suka kai Afrika ta Yamma, ya ma haura rabin adadin hare-hare 2,142 da ‘yan ta’addar suka kai a Afrika baki ɗaya, a cikin watanni ukun farkon shekarar 2024.

ISWAP sun kashe mutum 609 a hare-hare 609 da suka kai Najeriya, sai kuma Kamaru da suka ka kashe mutum 40.

ISGS kuwa ta kai hare-hare 73, inda ta halaka mutum 446 yankunan ƙasar Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar.

ISGS kamar yadda jadawalin ya nuna, ta kashe mutum 224 a Jamhuriyar Nijar, wasu 180 a Mali, sai kuma mutum 62 a Burkina Faso.

Can a ƙasar Kongo kuwa, ISCAP, wato ‘yan Boko Haram na Tsakiyar Afrika, sun kai hare-haren ta’addanci sau 135, suka halaka mutum 762.

Reshen IS na Zimbabwe kuwa sun ce sun kashe mutum 137 a hare-hare 68 da suka kai.

Haka nan a ƙasar Somaliya IS sun kashe mutum 128, suka kai hare-haren ta’addanci sau 14.

Kada a manta kuma akwai hare-hare na ta’addaci da ya haddasa asarar rayuka da IS ta nuna ita ce ta kai hare-haren a yankin Asiya, Turai da Gabas ta Tsakiya.

Jadawalin da IS ta fitar ya nuna cewa sun kashe mutum 500 a Rasha, wasu 393, a Siriya, sun kashe mutum 303 a Iran, Sai Pakistan inda suka kashe mutum 142, sai mutum 138 a Afghanistan, 96 a Iraqi, 33 a Philippines mutum 33, dai Turkiyya mutum biyu.

A hare-hare 788, “an kashe mutum 3,749, aka jikkata 51, cikin su har da sojojin Najeriya da kwamandojin su,” cewar rahoton ISWAP ɗin.

A cikin watanni ukun farkon shekarar 2024, “yan ta’addar sun banka wa gidaje 1,400 wuta, sun fasa kantina kamar yadda IS ta yi iƙirarin yin haka ɗin.

‘Yan ta’addar sun ce sun kai farmaki sau 47 kan coci da barikin sojoji.

Sun ce sun ƙone motoci 202, sun ƙwaci motoci 25 a matsayin ‘ganima’.

Sai kuma rahotanni sun nuna fiye da mutum miliyan 35 na neman tallafi saboda tashe-tashen hankula a yankin Tafkin Chadi, wanda ya haifar da asarar dubban rayuka.

People are also reading