Home Back

Turka-Turkar Shari’ar Masarautar Kano: Makiya Sarki Muhammad Sanusi II, Makiya Gwamnan Jihar Kano Da Kanawa, Murna Ta Koma Ciki, Daga Imam Murtadha Gusau

premiumtimesng.com 2024/7/3
Turka-Turkar Shari’ar Masarautar Kano: Makiya Sarki Muhammad Sanusi II, Makiya Gwamnan Jihar Kano Da Kanawa, Murna Ta Koma Ciki, Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh

Ya ku bayin Allah! Ku sani, fadar gaskiya, da tsayuwa a kan gaskiya da goyon bayan gaskiya da masu gaskiya wani babban al’amari ne wanda shari’ah tayi umurni da shi, kuma ta karfafa shi a cikin wannan al’ummah ta Annabi Muhammad (SAW), kuma ba kowa ne zaka samu da irin wannan matsayi ba, sai mutane masu imani, masu tsoron Allah kuma nagartattu, wadanda zuciyar su take wankakkiya daga dattin sharri, da hasada, da makirci da bakin ciki.

Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi umurni da haka a cikin littafinsa mai tsarki, inda yake cewa:

“Ya ku wadanda suka yi imani, kuji tsoron Allah kuma ku kasance tare da masu gaskiya.” [Suratu Taubah, 9:19]

A wannan aya ta Alkur’ani mai girma Allah Madaukaki yayi umurni akan goyon bayan gaskiya da masu gaskiya. Don haka duk wani mutumin kirki zaka same shi da wannan dabi’a mai kyawo. Kamar yadda duk wani mutumin banza, a duk inda yake, zaka same shi yana goyon bayan rashin gaskiya da marasa gaskiya.

Kuma su bayin Allah nagari, zaka same su suna goyon bayan gaskiyar da masu gaskiyar komai dacinta, kuma ko me za’a fada game da su, duk zagin da za’a yi masu, duk sunan da za’a kira su da shi, kai ko me zai faru, suna nan dai akan wannan matsayi nasu na goyon bayan gaskiya, saboda umurni ne daga Allah, kuma in dai lamari ya kasance umurnin Allah, to babu ruwansu da tsargin duk wani mai zargi, ko wanene.

Don haka, ya zama wajibi al’ummah ta kara sani cewa, duk wani mai goyon bayan sarautar Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammad Sanusi II, tare da goyon bayan matakin da Mai girma Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya dauka, na rusa kirkirarrun masarautu biyar, da dawo da Martabar jihar Kano, a bisa masarauta daya, kuma karkashin jagorancin Sarki guda daya, ya sani, wannan mutum yana kan hanya, kuma yana kan daidai. Kuma ya sani, yana kan goyon bayan gaskiya ne da masu gaskiya. Don haka, wannan mutum kar ya damu, kar yayi shakkar komai, kuma kar ya yarda wani mutum yayi masa wata barazana, ko ya zare masa ido.

To wanda ma baya kan gaskiya, kuma yana sane amma ya take sani, yayi rashin kunya da rashin mutunci, bare kai da kasan kana akan gaskiya.

‘Yan uwa masu girma, duk wanda yake bin lamurran da suke faruwa a kasar nan sau da kafa, kuma yake bibiyar irin abubuwan da suke faruwa a arewa, da turka-turka da rigingimun da suke faruwa a masarautar jihar Kano, to lallai zai ga abubuwan takaici da ban mamaki da ban haushi, kai har da ma abubuwan ban dariya da na jahilci.

Jiya Alhamis, 20/06/2024, babbar kotun tarayya da ke birnin Kano, karkashin jagorancin Alkali Muhammed Liman, ta yanke wani hukunci, wanda kawai nan take, sai muka ga duk wasu makiyan al’ummar jihar Kano masu daraja, da makiyan Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammad Sanusi II, da makiyan mai girma Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga cikin ‘yan jaridu da sauransu, nan take suka hau soshiyal midiya, suka buga a jaridunsu, suna ta yada wata karya, suna ta murna, WAI KOTU TA SOKE NADIN DA AKA YIWA SARKI SANUSI NA BIYU.

Kuma wallahi wadannan makiya, masu kiyayya da Sarki Sanusi da Gwamna da jihar Kano, da zaka bibiyi dukkanin ra’ayoyansu, wallahi zaka tarar ba komai yasa suke wannan ba illa hasada da bakin ciki. Wadannan mutane suna tuhuma kuma suna jayayya da abun da Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi na daukaka darajar wasu bayi daga cikin bayinsa. Don haka sun sha alwashin cewa, wane ba zai yi ba, sai wane. Kai kace sune masu yi ba Allah ba.

A suruttan su, sun nuna su Musulman kwarai ne, masu imani da Allah da kaddararsa, amma dukkanin ayukkansu sun nuna sabani da akasin hakan.

A iya rashin hankali irin nasu, sun sha alwashin cewa sai sun nunawa Allah bai isa ba da ya daukaka darajar su wane.

Ya ku al’ummah, wadannan mutane masu jayayya da Allah, bayan sun gama murnarsu a bisa jahilci da rashin sanin doka da hukuncin kotu, sai daga baya, bayan an fassara masu abunda wannan hukunci yake nufi, nan take sai kuma suka yi tsit, murna ta koma ciki, sai ido ya raina fata.

Kawai a bisa jahilci irin nasu, wai su so suke yi kotu tace Sanusi fito, Aminu shiga. Ko kuma Sanusi sauka, Aminu hawo. Haba jama’ah ai kun ga wannan ba wani abu ya jawo wannan ba in ban da hasada da jahilci.

Abunda wannan hukunci na wannan kotu yake nufi shine: rusa masarautu biyar dai da mai girma Gwamna yayi yana bisa ka’ida, kuma suna nan a rusassunsu. Domin kundin tsarin mulki ya ba wa Gwamna karfi da ikon yin hakan. Kuma dokar da majalisar dokokin jihar Kano tayi ita ma tana nan daram, kuma Sarki Sanusi yana nan daram a matsayin halastaccen Sarkin Kano. Kawai abunda ya ruda wadancan makakkun mutane shine, cewar da alkali yayi, idan dai har nadin Sarki Sanusi anyi shi ne bayan ya bayar da umurnin tsayawa a inda ake, to nadin da Gwamna yayi masa an rusa shi.

To alhamdulillah, muna godiya ga Allah da ya kaddari cewa, alkalin ya bayar da wancan umurni ne bayan an nada Sarki Sanusi a matsayin Sarkin Kano. To kun ga anan, wannan umurni ba zai taba shafar nadin da Gwamna yayi wa Sarki Sanusi a matsayin halastaccen Sarkin daular masarautar Kano ba.

Don haka sai murnar makiya nan take ta koma ciki.

Irin abun nan ne da masu karin magana suke cewa: YARO BARI MURNA, KAREN KA YA KAMA ZAKI.

Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da doka ranar 23 ga watan biyar 2024, gwamna ya sa wa dokar hannu, kuma ya zabi Sarki Sanusi a matsayin halastaccen Sarkin daular masarautar Kano duk dai a ranar. Anyi umurnin kotun tarayya ranar 24 ga watan biyar 2024, wanda ita kuma gwamnatin jihar Kano a hukumance ba’a sanar da ita wannan umurnin ba sai a ranar 27 ga watan biyar 2024, kamar yadda shi alkalin da kan sa ya tabbatar da hakan.

To kamar yadda alkalin ya nuna cewa, duk wani abu daya biyo bayan umurnin da yayi na ranar 24 ga watan biyar 2024 an soke shi, wannan babu wata matsala akai, domin babu abunda aka yi ranar 24 ga watan biyar 2024 illa bukin gabatar da Sarki ba nada shi ba.

Hukuncin ma da masana shari’ah da masana dokokin kasa da tsarin mulkin kasa, irin su Farfesa Auwal Yadudu da Mista Femi Falana da sauran ire-irensu duk sun soke shi. Ma’ana irin yadda alkalin yake ta dambarwa da tufka-da-warwara, kawai dai domin ya faranta wa wasu rai, amma da yake Allah ba azzalumi bane, kuma ba zai taba goyon bayan zalunci da azzalumai ba, sai ga shi dai duk da haka, Allah ya dora mu akan su.

Don haka alhamdulillah, alhamdulillah, alhamdulillah. Mu munyi imani da Allah, kuma muna nan a bisa goyon bayan gaskiya da masu gaskiya.

Don haka, mahassada wallahi sai dai ku mutu da bakin ciki, Muhammad Sanusi ll har gobe shine halastaccen Sarkin Kano, wanda al’ummar jihar Kano suke so kuma suke kauna. Kuma wallahi, duk wani yunkuri na dora masu wani mutum wanda basu so, a matsayin Sarki, wallahi mun yi imani ba zasu ci nasara ba, kuma wannan yunkuri zai hadu da cikas, zai hadu da matsala, kuma zai hadu da fushin ilahirin Kanawa, da al’ummar jihar arewa masu kishin yankin su.

Kuma tabbas, zamu kalubalanci duk wani katsalandan da wasu zasu yi muna a yankin mu na arewa, wanda baza su iya yin sa ba a nasu yankin.

Kuma don Allah wace kotu ce, kuma wane alkali ne zai iya yanke hukuncin da zai kakaba wa mutane abun da basa so?

Sannan domin Allah duk Najeriya, kai duk ma duniya, wane Gwamna ne zai iya yin aiki tare da mutumin da yasan baya son sa, kuma baya kaunarsa, kuma mutumin da yake yi masa zagon-kasa da makarkashiya? Mutumin da yake sa ‘yan daba da ‘yan iska suna zaginsa?

Don haka Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, yana so ne ya dawo wa da jihar Kano Martabar ta da matsayin ta na Sarki daya al’ummah daya, matsayin da shine suka gada kaka-da-kakanni. Matsayin da zai hada kan al’ummar Kanawa, kowa yaso juna ya kaunaci juna. Kuma yana so ne yayi aiki tare da Sarkin da yake son sa, kuma yake kaunarsa; Sarkin da ba zai yi masa wata makarkashiya ba, wanda ba zai hada kai da abokan adawa a cutar da shi ba, kuma wanda zai bashi cikakken hadin kai suyi aiki tare, domin ciyar da jihar Kano gaba.

Don Allah ta yaya Gwamna zai iya yin aiki tare da mutumin da yake yakarsa? Mutumin da tun lokacin zabe, har zuwa maganar kotu, kowan yasan irin rawar da ya taka wurin tadiye Gwamna da cin mutuncinsa, amma wai wannan ne wasu mutane suke son wai lallai sai Gwamna yayi aiki tare da shi a matsayin Sarki, kawai ba don komai ba, sai don suci gaba da ayukkan su na rusa jihar Kano da al’ummar Kanawa a siyasance!

Haba jama’ah, wadannan mutane, ai suma sun san wannan ba zai yiwu ba wallahi.

Daga karshe, ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala yaci gaba da taimakon gaskiya da masu gaskiya a koda yaushe. Allah yaci gaba da taimakon kasar mu Najeriya, da yankin mu na arewa da jihohin mu baki daya, amin.

Wassalamu alaikum,

People are also reading