Yaron Tsohon Gwamna Ya Jagoranci Zanga Zanga, Ya Nemi Tinubu Ya Sauka Daga Mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kaduna - Kasim Balarabe Musa ya jagoranci wata zanga-zangar lumuna da aka shirya domin kokawa da halin da al’umma ke ciki.
An yi wannan zanga-zanga ne a ranar 12 ga watan Yuni yayin da ake bikin zagayowar ranar murnar dawowa mulkin damukaradiyya.
Kasim Balarabe Musa ya jagoranci wannan zanga-zangar lumuna ne a garin Kaduna kamar yadda Vanguard ta kawo labarin a makon nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen wannan zanga-zanga ne Kasim Balarabe Musa ya yi Allah-wadai da gwamnatin APC da ke mulki karkashin Bola Ahmed Tinubu.
Kasim Balarabe Musa yana cikin ‘ya ‘yan Balarabe Musa wanda ya yi mulki a jihar Kaduna.
Marigayi Balarabe Musa ya zama gwamna a karkashin jam’iyyar PRP mai adawa a 1979, daga baya rikicin siyasa ya jawo aka tsige shi.
A cewar Kasim Balarabe Musa, tun da shugaban kasa Bola Tinubu ya shiga ofis a 2023, babu wani abin alfahari da za a nuna a mulkinsa.
Matashin ya fadawa ‘yan jam’iyyar PRP cewa Najeriya ta ci-baya a karkashin mulkin APC.
Kasim ya ce mahaifinsa da irinsu Cif Gani Fawehinmi SAN da Shehu Sani sun yi kokari wajen ganin an dawo mulkin farar hula a Najeriya.
A yau, yana ganin kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba ganin yadda ake fama da tsadar rayuwa a hannun wadanda suka canji sojojin.
Punch ta rahoto shi yana cewa talakawa ba su iya cin abinci duk da arzikin kasar nan baya ga kashe-kashe da tabarbarewar al’amura.
Kasim Musa ya ba shugaba Bola Tinubu shawarar ya canza dabarunsa ta yadda za a iya magance matsalolin da suka addabi Najeriya.
Idan kuwa kalubalen sun fi karfin Tinubu, ya nemi shugaban kasar ya yi murabus domin wannan ne mafi munin lokaci tun 1960.
A jihar ta Kaduna, an ji labari tsohon shugaba a jam’iyyar APC ya yi hasashen Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani za su rasa tazarce a 2027.
Alhaji Salihu Muhammad Lukman ya ce wani babba a APC ya hada-kai da fadar shugaban kasa a yaki Mal. Nasir El-Rufai saboda siyasa.
Asali: Legit.ng