Home Back

Tinubu Ya Kau da Kai Ga Rikicin Sarautar Kano, Zai Yi Jawabi Ga Majalisun Tarayya 2 a Abuja

legit.ng 2024/9/29
  • Ana tsaka da rikicin sarautar jihar Kano, Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga taron majalisun Tarayya guda biyu
  • Tinubu zai yi magana ne kan nasarar dimukradiyya shekaru 25 da majalisar Tarayya ba tare da katsalandan ba
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya nemi alfarma gun Tinubu na tsoma baki a rikicin sarautar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu zai yi jawabi ga majalisun Tarayya guda biyu a gobe Laraba 29 ga watan Mayu.

Tinubu zai yi wa majalisun jawabi a tare game da nasarar dimukradiyya shekaru 25 da kuma nasarar kasancewar majalisun ba tare da matsala ba.

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, Tinubu zai yi jawabi ga majalisun Tarayya
Bola Tinubu zai gana da majalisun Tarayya 2 ana tsaka da rigimar sarautar jihar Kano. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu. Asali: Twitter

Tinubu zai kaddamar da sabon dakin karatu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Sani Tambuwal ya fitar a jiya Litinin 27 ga watan Mayu, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tambuwal ya ce yayin taron, Tinubu zai kaddamar da sabon ƙayataccen dakin karatu da aka samar a cikin majalisar, Channels TV ta tattaro.

"Ana sanar da sanatoci da mambobin majalisar dokoki cewa akwai taron murnan cika shekaru 25 na kasancewar dimukradiyya da majalisar Tarayya."
"Bola Tinubu zai yi jawabi na musamman ga taron majalisun guda biyu a gobe Laraba 29 ga watan Mayu."
"Ana bukatar dukkan mambobin majalisun biyu da su samu wurin zama da misalin karfe 9:00 na safe."

- Sani Tambuwal

Mafi yawanci irin wannan jawabi ga majalisun biyu a tare ana yi ne kawai lokacin gabatar da kasafin kudi a kasar.

Kano: Abba ya nemi alfarmar Tinubu

Wannan taro da Tinubu zai gabatar na zuwa ne yayin da ake tsaka da rikicin sarautar jihar Kano fiye da kwanaki biyar.

Ana zargin Gwamnatin Tarayya da hannu a ruruta rikicin sarautar jihar tun bayan tube Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna guda hudu.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin hannu a dagulewar rikicin sarautar jihar da ya ki ci ya ki cinyewa.

Abba Kabir ya nemi alfarma gun Tinubu

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nemi alfarma gun Shugaba Bola Tinubu kan rikicin sarautar jihar.

Abba ya bukaci Tinubu da ya tsoma tare da fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga jihar domin samun zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

People are also reading