Home Back

Manoma Na Bukatar A Yi Rangwamen Kayan Aikin Noma – Wasu Jami’ai

leadership.ng 2024/8/24
IFAD

Babban Sakatare a Ma’aikatar Aikin Noma ta Jihar Neja, Dakta Mathew Ahmed, ya yi kira da a samar wa da manoman jihar rangwamen farashin takin zamani da sauran kayan aikin noma, don samar da wadataccen abinci, duba da karancin abinci da ake a ci gaba da fuskanta a wannan kasa.

A hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Minna, babban birnin jihar; Mathew ya yi nuni da cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta rage wa manoman kasar farashin takin zamani tare kuma da samar musu da kayan aikin noma, wanda ya ce; yin hakan zai bai wa manoman damar shafe shekara guda suna yin noma.

Kazalika ya yi nuni da cewa, samar wa da moman kayan aikin noman rani sau uku a shekara, zai taimaka wajen kara samar da wadataccen abinci da kuma kara habaka tattalin arzikin wannan kasa baki-daya.

Haka zalika sanar da cewa, Gwamnatin Umaru Bago; tuni ta bazama wajen farfado da aikin noma a jihar, inda ta samar da taraktocin noma guda 1,000, injinan aikin noma guda 10,000 da sauransu ga manoman jihar.

Bugu da kari ya kuma kara da cewa, gwamnatin ta kuma samar da injinan yin girbi guda 100 da sauran kayan aikin noma, don bai wa mata da matasan jihar damar rungumar akin noma.

Ya ci gaba da cewa, gwamnati ta kuma samar da guraren yin noman ranin na gwaji guda 100, inda ya sanar da cewa; a yanzu haka gwamnatin na kan noma hekta miliyan daya, wanda a kowace karamar hukuma guda a jihar; aka ware mata hekta 10,000.

Sannan, a kan kokarin da gwamnatin jihar ke yi na magance kalubalen rashin tsaro ya ce, Gwamnan Jihar ya kirkiro da ma’aikatun kula da gonaki tare da samar da tsaro da kuma ta kula da harkokin makiyaya, musamman domin dakile rikicin manoma da makiyaya a fadin jihar.

Ya kara da cewa, kirkiro da wadannan ma’aikatu ko shakka babu; za su taimaka wajen tabbatar da bayar da kariya ga al’ummomin da ke a jihar daga hare-haren ‘yan bindiga da kuma satar mutane, a daukacin kananan hukumomi 25 na jihar.

Kazalika ya ci gaba da cewa, Gwamnan Jihar na ganawa da Sarakunan Gargajiya akai-akai, domin duba a kan kalubalen rashin tsaron; ya kuma kara karfafa kungoyin tsaro na sa kai, yadda za su yi aiki tare da hukumin  tsaro kafada da kafada, domin manoman jihar su samu damar noma gonakinsu tare kuma da kara magance kalubalen rashin wadataccen abinci a jihar.

A kokarinta na magance karancin abinci, Gwamnatin Jihar Nassarawa ta bayyana cewa, ta fara noman Shinkafa, Kantu, Gero da kuma Masara kimanin hekta 10,000 a yankin  Jangwa da ke          Karamar Hu

Gwamnatin tarayya ta sanya matasa 200 cikin shirinta na bunkasa noma, wanda ake kira da ‘ATASP-1’.

Matasan da za su amfana da wannan shiri, an zabo su ne daga sassa daban-daban guda hudu na fadin kasar nan.

Jami’in shirin na kasa, mai kula da shiyoyin Jihohin Kano da Jigawa; Dakta Ibrahim Muhammed Arabi ne, ya sanar da hakan a lokacin bude taron shirin.

Arabi, wanda jami’in da ke kula da aikin noma; domin riba na kasa kan shirin, Dakta Kunle Alege ya wakilce shi a wajen taron; ya ce a karkashin shirin za a horas da matasa 50 wadanda aka zabo daga kowace shiyya guda ta kasar nan, wanda hakan ya sanya adadin matasan suka kai 200.

Ya kara da cewa, za a koyar da matasan yadda za su aiwatar da noman, don kasuwancin zamani tare kuma da yin amfani da dabarun zamani; domin cimma nasarar shirin.

A cewarsa, bayan an horar da matasan za kuma ci gaba da biyan su tare da tallafa masu da kudade; domin samun damar gudanar da aikin yadda ya kamata.

Shi ma wani jami’i, a sashen cibiyar aikin noma ta (IITA), Dakta Alpha Kamara ya bukaci matasan da su yi amfani da horon da aka ba su, don zama masu dogaro da kawunansu ta hanyar aikin noma.kumar  Awe ta jihar.

Gwamnan Jihar, Abdullahi Sule ne ya sanar da hakan jim kadan bayan ya duba aikin, inda ya bayyana cewa; aikin na daya daga cikin ajandar shirin Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu na samar da tsaro.

Sule ya sanar da cewa, Allah ya albarkaci Jihar Nassarawa  da kasar noma mai matukar kyawun gaske, wanda hakan ya sa al’ummar jihar ke yin noma; don zama masu dogaro da kawunansu.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, ana yin aikin ne a karkashin shirin gwamnatin na  bunkasa aikin noma wato (NADP).

Sule ya kara da cewa, za a sanya manoman jihar a cikin tsarin aikin noman, wanda hakan zai ba su damar samun ingantaccen Irin noma da sauran kayan aikin noma.

People are also reading