Home Back

NEJA A HANNUN BOKO HARAM: ‘Yan ta’adda sun yi wa matasa 10 yankan-rago, sun guntule kawunan su

premiumtimesng.com 2024/6/26
A karo na biyu cikin mako daya, Boko Haram sun afkawa kauyen Gubio, sun kashe mutum 31

‘Yan ta’addar Boko Haram sun yi wa mutum 20 kisan-gillar wulaƙanci a Jihar Neja.

Lamarin ya faru a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro, cikin garin Bassa, inda su ka yi wa matasa 10 yankan-rago, saboda ‘yan ta’addar sun nemi matasan su jone da su, su shiga Boko Haram, amma sun ƙi amsa tayin da aka yi masu.

Wani ganau wanda ya nemi kada a bayyana sunan sa, ya shaida wa wakilin mu cewa an guntule kawunan matasan, bayan an yi masu yankan rago.

Wani ɗan garin da ya arce ya kuɓuta da kyar, ya shaida cewa ‘yan ta’addar sun tilasta wa mutanen garin riƙe kawunan matasan da suka guntule, su kuma su na ɗaukar bidiyon su.

‘Yan ta’addar sun afka cikin garin Bassa da rana tsaka, a ranar Alhamis, inda suka tattara mutanen garin da suka ritsa, suka ware matasa baligai 20, sannan suka buɗe masu wuta.

“Sun shaida mana cewa duk wanda ya ƙi shiga Boko Haram, za a yi masa irin kisan da suka yi wa waɗanda suka kashe ɗin.

“Sun ce sun ware mutum 10 duk matasa sun yi masu yankan rago, kuma sun guntule kawunan su, domin hakan ya zama darasi ga duk wanda ya ƙi bin umarnin su.

“Sun ce wai sun yi mana haka, saboda a baya sun ce kowa ya fice daga ƙauyen, amma mun ƙi ficewa. Wato ko dai mu jone da su, ko kuma mu bar garin.” Inji wani mazaunin Bassa.

Sauran ƙauyukan da aka kai wa hari a ranar Juma’a, sun haɗa da Lanta, Kasimani, Unguwan-Madi da Makuda. A waɗannan ƙauyuka sun banka wa gidaje wuta, kuma sun kashe dabbobi.

Idan ba a manta ba, watanni biyu da suka gabata, Boko Haram sun yi wa mutum 9 yankan rago a Allawa, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro, bayan sun tarwatsa sansanin sojojin da ke ƙauyen.

“Waɗanda aka yi wa yankan ragon dai an kashe su ne, saboda sun ƙi bin umarnin Boko Haram da suka ce duk wanda ya gudu daga garin, to kada ya koma.

“Su kuma sun koma ne domin su samo abinci. Da aka kashe su, sai aka ce wa matan su da suke tare, su wuce gida kowa ya je ya kai labarin abin da ya faru.”

Har yanzu ba a ji komai daga Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ba.

Amma sanata mai wakiltar Neja ta Gabas, Sani Musa, ya bayyana mummunan kisan mutum 20 a Bassa da ce dabbanci ne, rashin imani ne. Kuma ya miƙa ta’aziyyar ga iyalan mamatan.

A yankin ne dai cikin makonni biyu da suka gabata mahara suka tafi da mutum 160 daga garin Kuchi, kuma har yau babu labari.

People are also reading