Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Haba Gwamnoni, ku bari a bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kan su kawai

premiumtimesng.com 2024/6/26
Masu riƙe da sarautun gargajiya da shugabannin yankunan karkara ke mara wa ‘yan bindiga baya – Gwamnonin Arewa maso Gabas

Kwanan nan tirka-tirka da ƙaƙudubar kayan-tsayen da gwamnonin Najeriya ke yi wa ‘yancin ƙananan hukumomi zai zama abin tirja-tirja a Kotun Ƙoli. Saboda Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya shigar da ƙara, a madadin Gwamnatin Tarayya, a Kotun Ƙoli, inda yake neman a kuɓutar da ƙananan hukumomi 774 daga hawan-ƙawarar da gwamnoni ke yi masu ta fuskar yin yadda suka ga dama da kuɗaɗen su da kuma yin yadda suka ga dama wajen cire shugabannin ƙananan hukumomi, ko gudanar da zaɓen ɗauki-ɗora ko naɗa shugabannin riƙon-ƙwarya. Muna maraba da wannan ƙara da aka maka gwamnonin Najeriya.

Wasu gwamnonin ma saboda tsananin yi wa doka karan-tsaye, har su gama wa’adin shekaru huɗu ko shekaru takwas ba su yin zaɓe, sai dai su naɗa wa kowace ƙaramar hukuma shugaban riƙo.

A cikin shekaru 12 zuwa 2019, ƙididdigar da Dataphyte ya fitar wadda PREMIUM TIMES ta wallafa, ta nuna cewa an bai wa ƙananan hukumomi naira tiriliyan 15.5. Amma yawancin kuɗaɗen nan duk gwamnoni sun karkatar da su, ko kuma sun watsa su aljifan su.

Cikin watan Afrilu 2024 Kwamitin Rarraba Arzikin Ƙasa (FAAC) ya raba wa ƙananan hukumomi Naira biliyan 293.816, yayin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauki naira bilyan 390.412, su kuma jihohi aka raba masu Naira biliyan 403.4.

Gwamnoni baya ga taɓa kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi, su na kuma zabtare kashi 10 bisa 100 na kuɗaɗen haraji, wanda ɗaya ne daga cikin dalilan da ya sa suka ƙirƙiri Asusun Haɗin-gwiwa na Jihohi da Ƙananan Hukumomi kenan.

Domin magance wannan kwatagwangwama, Gwamnatin Tarayya na neman Kotun Ƙoli ta bada odar hana jihohi yi wa ƙananan hukumomi katsalandan da a fannin kuɗaɗen su, wato a riƙa bai wa kowace ƙaramar hukuma kuɗaɗen ta kai-tsaye, ba ta hannun gwamnatin jiha ba.

A ƙarƙashin Kundin Tsarin Dokokin Najeriya, gina kasuwa da kula da kasuwanni, tashoshin mota, makarantun firamare, harkar shara, cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko, harkar zirga-zirga, gyaran ƙananan titina, kula da maƙabartu da mayanka dabbobi duk ayyukan ƙananan hukumomi ne. Amma duk sun daina, saboda ba a ba su kuɗaɗen, duk gwamnoni sun riƙe.

Rashin gudanar da waɗannan ayyuka ya haifar da zaman-dirshan ga ɗimbin ma’aikatan ƙananan hukumomi, waɗanda ba su komai sai dai zuwa karɓar albashi kaɗai a ƙarshen wata. Yanzu ma sun daina zuwa karɓa, saboda kowa alat ya ke gani a asusun bankin sa.

Tun daga 1999 ake ƙadabolo da Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi (ALGON) kan wannan bambarwa. Amma har yau kusan sun gaji sun kusa haƙura, ba su yi nasara ba.

Ba za mu ci gaba da kafa gwamnoni su na zama wasu fir’aunoni ba, su na toshe wa ‘yan majalisar dokokin su baki da kuɗaɗe su karkatar da tsarin dimokraɗiyya. Su na yin yadda suka ga dama a jiha, kuma su yi abin da suka ga dama a ƙananan hukumomi.

People are also reading