Home Back

Zamfara: Malamin Addini Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Shafe Kwanaki a Hannun Yan Bindiga

legit.ng 2024/8/21
  • Babban malamin addinin Kirista a jihar Zamfara, Mikah Sulaiman ya samu kubuta daga hannun yan bindiga bayan makonni
  • Daraktan yada labaran cocin Katolika Diocese a Sokoto, Pascal Salifu ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a jiya Lahadi
  • A makonni biyu da suka wuce ne aka sanar da cewa yan bindiga sun sace babban malamin a Gusau da ke jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Rahotanni sun yi nuni da cewa babban malamin addinin Kirista da aka kama ya samu ƙubuta.

Yan bindiga sun sace Rabaran Mikah Sulaiman ne makonni biyu da suka wuce a karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Rabaran Sulaiman MiKah
Malamin addini ya kubuta daga hannun yan bindiga a Zamfara. Hoto: Catholic Diocese of Sokoto Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Daraktan yada labaran Cocin Katolika Diocese na jihar Sokoto ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe 'yan bindiga su ka kama malamin?

A ranar 22 ga watan Yuni ne rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa an cafke Rabaran Mikah Sulaiman a cikin gidansa.

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ba ta samu bayani daga hukumar cocinsa ba amma dai labarin ya risketata ta wasu hanyoyi.

'Yan bindiga: Malamin addini ya kubuta

A jiya Lahadi ne cocin Katolika Diocese ya fitar da sanarwar kubutar Rabaran Mikah Sulaiman daga hannun yan bindiga.

Hukumar cocin ta mika godiya ga jami'an tsaro da dukkan waɗanda suka sanya hannu wajen ganin malamin ya kubuta.

A sanya malamin addini a addu'a

Har ila yau hukumar cocin Katolika Diocese ta bukaci al'umma su cigaba da yiwa Rabaran Mikah Sulaiman addu'a, rahoton Channels Television.

Hakan na zuwa ne bayan bayyana cewa a halin yanzu malamin yana kokarin murmurewa ne daga halin da ya samu kasa a ciki yayin da aka kama shi.

An yi garkuwa da basarake a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun yi awon gaba da dagacin Tunburku, Malam Ashiru Sharehu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun tafi da basaraken a lokacin da ya kamo hanyar dawowa gida daga gonarsa.

Asali: Legit.ng

People are also reading