Zamfara: Malamin Addini Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Shafe Kwanaki a Hannun Yan Bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Rahotanni sun yi nuni da cewa babban malamin addinin Kirista da aka kama ya samu ƙubuta.
Yan bindiga sun sace Rabaran Mikah Sulaiman ne makonni biyu da suka wuce a karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Daraktan yada labaran Cocin Katolika Diocese na jihar Sokoto ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 22 ga watan Yuni ne rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa an cafke Rabaran Mikah Sulaiman a cikin gidansa.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ba ta samu bayani daga hukumar cocinsa ba amma dai labarin ya risketata ta wasu hanyoyi.
A jiya Lahadi ne cocin Katolika Diocese ya fitar da sanarwar kubutar Rabaran Mikah Sulaiman daga hannun yan bindiga.
Hukumar cocin ta mika godiya ga jami'an tsaro da dukkan waɗanda suka sanya hannu wajen ganin malamin ya kubuta.
Har ila yau hukumar cocin Katolika Diocese ta bukaci al'umma su cigaba da yiwa Rabaran Mikah Sulaiman addu'a, rahoton Channels Television.
Hakan na zuwa ne bayan bayyana cewa a halin yanzu malamin yana kokarin murmurewa ne daga halin da ya samu kasa a ciki yayin da aka kama shi.
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun yi awon gaba da dagacin Tunburku, Malam Ashiru Sharehu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun tafi da basaraken a lokacin da ya kamo hanyar dawowa gida daga gonarsa.
Asali: Legit.ng