Home Back

Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi Ya Karbi Bakuncin Babban Malami a Fadarsa

legit.ng 2024/7/5

Kano - Babban malamin addinin Musulunci a Maidugurin jihar Borno, Khalifa Sheikh Ali Abulfatahi ya ziyarci mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Sarkin ya karɓi bakuncin fitaccen malamin da ƴan tawagarsa a fadarsa da ke Ƙofar Kudu a cikin kwaryar birnin Kano.

Hakan na ƙunshe ne a wani saƙo da masarautar Kano ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.

"Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi ll CON, ya Karbi bakuncin Khalifa Sheikh Ali Abulfatahi daga Maiduguri."

Asali: Legit.ng

People are also reading