Home Back

Sadaukar Da Kai Ga Hidimtawa Jama’a: Tasirin Mahaifin Xi Jinping A Kan Dansa

leadership.ng 2024/7/6
Sadaukar Da Kai Ga Hidimtawa Jama’a: Tasirin Mahaifin Xi Jinping A Kan Dansa

Kalamai da ayyukan mahaifin Xi Jinping, Xi Zhongxun, sun darsu cikin rayuwar shugaban kasar Sin da ayyuka da tunaninsa, lamarin dake ba shi kwarin gwiwar sauke nauyin da ya rataya a wuyanshi na tafiyar da harkokin kasa da na al’umma.

Jim kadan bayan kama aiki a matsayin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na yankin Suide, Xi Zhongxun ya gabatar da bukatar “hidimtawa mutane 520,000” tare da tabbatar da cewa shi da ma’aikatan kwamitin jam’iyya na yankin Suide, sun samar da abun koyi.

A don haka, ya nemi mambobin jam’iyyar a dukkan matakai da kada su zama jami’ai ko shugabanni, wato su bar zaman ofis su shiga can cikin kauyuka domin hidimtawa jama’a a aikace.

A kowanne mataki na aikinsa na juyin juya hali, Xi Zhongxun ya kan kwatanta rayuwar jama’a a kansa. Daga shawo kan matsalolin samar da kayayyaki da na rayuwar masu kaura zuwa kudu, zuwa ba lardin Guangdong na kasar Sin damar jagorantar aikin raya tattalin arziki, ya kan gudanar da ayyuka ne daga mahangar kare muradun jama’a.

Ba tare da la’akari da matsayinka ba, ka jajirce wajen hidimtawa jama’a, ka yi la’akari da muradun jama’a da zuciya daya, ka yi mu’amala sosai da su, kuma ya zamanto mutane za su iya samunka a ko da yaushe,” kalaman Xi Zhongxun ke nan ga dansa.
Bisa tunawa da kalaman mahaifinsa, Xi Jinping ya ziyarci yankuna 14 masu fama da matsananciyar fatara, bayan ya zama sakatare janar na kwamitin kolin JKS a watan Nuwamban shekarar 2012. Ya ziyarci kauyuka da iyalai, ya kuma shaidawa al’ummomi cewa shi “hadimin jama’a” ne.

Yayin rangadi a cikin gida, Xi ya kan tattauna da mazauna, ya tambaye su yanayin rayuwarsu da jaddadawa sauran jami’ai nauyin dake tattare da hidimtawa jama’a.

Mutanen biyu daga zamani biyu, suna da kuduri iri daya, kuma suna daukar muradin jama’a na samun kyautatuwar rayuwa a matsayin babban buri.

People are also reading