Home Back

Fyade: An Yanke Wa Robinho Zaman Gidan Kaso Na Shekara Tara

leadership.ng 2024/5/17
Fyade: An Yanke Wa Robinho Zaman Gidan Kaso Na Shekara Tara

Wata kotu a kasar Brazil ta sanar da cewa tsohon dan kwallon Manchester City da Real Madrid, Robinho, zai yi zaman gidan kaso na tsawon shekara tara sakamakon hukuncin laifin yin fyade.

An samu Robinho mai shekara 40 da laifi a wata kotu a Italiya a shekara ta 2017, wanda yana cikin taron dangin fyaden da aka yi wa wata mata ‘yar Albania ‘yar shekara 22.

Dan kwallon yana zaune a Brazil, wanda ba a mika shi Italiya ba, to amma alkalai a Brazil sun yanke hukunci ranar Laraba cewar zai yi zaman yari a kasar kamar yadda Italiya ta bukata.

Lauyoyi sun ce yana da lokacin da zai daukaka kara kafin hukuncin ya fara aiki a kansa amma idan har lokaci ya wuce ko kuma ya yanke shawarar ba zai daukaka kara ba to hukuncin zai fara aiki.

Tsohon dan wasan tawagar Brazil din da ya buga wa kasar wasa 100, yana buga wasa a kungiyar kwal-lon kafa ta AC Milan ne a lokacin da aka aikata laifin da aka zarge shi da yi.

A shekarar 2020 aka samu dan wasan da laifin aikata fyaden, bayan da ya yi rashin nasarar daukaka kara, inda wata kotu a Italiya ta tabbatar masa da hukuncin, sai dai daga nan ne masu shigar da kara a Italiya suka mika takardun izinin kamo shi daga Brazil. Robinho wanda ya yi kakar wasa biyu a Manchester City, ya sanar da wani kamfanin dillacin labarai a Brazil cewar da amincewar matar aka yi lalata da ita ba fyade aka yi mata ba.

Dan wasan ya dauki kofin La Liga biyu a kaka hudun da ya yi a Real Madrid daga nan ya koma kungiyar Manchester City a matakin wanda aka saya mafi tsada a Burtaniya kan kudi fam miliyan 32.5.

An kuma sayi dan kwallon a ranar karshe da za a rufe kasuwar cinikin ‘yan kwallo a Satumbar shekara ta 2008 – kuma a karon farko da Sheikh Mansour ya fara aiki a matakin wanda ya mallaki Manchester City.

Bayan kakar wasa biyu da Manchester City daga nan ya koma AC Milan, kungiyar da ya yi kaka biyar daga nan ya koma kasar China a kungiyar kwallon kafa ta Guangzhou Ebergrande inda bayan da ya bar China ne sai ya koma kungiyar Atletico Mineiro a Brazil.

People are also reading