Home Back

Yan Sanda sun Tarwatsa Sansanin 'Yan Ta'adda a Abuja, an Kama Miyagu

legit.ng 2024/7/3
  • Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun samu nasarar kai farmaki sansanin 'yan ta'adda da ke wasu dazukan da ke iyaka da jihar Kaduna
  • Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, SP Josephine Adeh ce ta tabbatar da samamen a sakon da ta fitar yau Lahadi inda ta ce jami'an DSS sun taimaka wajen aikin
  • Yayin samamen, an cafke wasu matasa hudu da su ka amsa cewa su ne miyagun da su ka addabi mazauna birnin tarayya Abuja da sace-sacen kudin fansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Rundunar 'yan sandan Najeriya hadin gwiwa da mafarauta daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun fatattaki wasu sansanin 'yan ta'adda dake dazukan Gidan Dogo and Kweti Forest a iyakar Kaduna da Abuja.

Jami'an tsaron sun samu gagarumar nasara inda su ka cafke akalla miyagu hudu, da su ka hada da Yahaya Abubakar mazaunin Mpape, Mohammed Mohamed mazaunin Zuba, Umar Aliyu da Nura Abdullahi mazauna dutsen Zuba Kubwa.

Police
Jami'an tsaro sun tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Abuja Hoto: Nigeria Police Force Asali: Facebook

A sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafinsu na facebook, rundunar ta bayyana cewa wasu bayanan sirri ne su ka taimaka mata wajen kai samamen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ceto wadanda aka sace

Channels Television ta tatattaro cewa jami'an tsaro sun tarwatsa sansanin 'yan ta'addan da su ka addabi al'umar birnin tarayya da kewaye.

Wadanda aka kama sun bayyana cewa su 'yan kungiyar ta'addancin da ake kira ‘Mai One Million’ ne, kuma sun dade su na satar mutane a Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandan 'yan sandan, SP Josephine Adeh ta tabbatar da ceto wasu da jama'a da miyagun su ka yi garkuwa da su, kuma an sada su da iyalansu.

Rundunar ta jaddada aniyarta na rubanya kokari domin tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.

'Yan ta'adda sun kai hari Taraba

A wani labarin kuma kun ji cewa 'yan ta'adda sun kai mummunan hari karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba inda su ka yi barna matuka,

Mutane kimanin 11 'yan ta'addan su ka kashe a harin, yayin da mutane da dama su ka samu raunuka lokacin da su ke kokarin tsira da rayukansu.

Asali: Legit.ng

People are also reading