Yan Sanda sun Tarwatsa Sansanin 'Yan Ta'adda a Abuja, an Kama Miyagu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Rundunar 'yan sandan Najeriya hadin gwiwa da mafarauta daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun fatattaki wasu sansanin 'yan ta'adda dake dazukan Gidan Dogo and Kweti Forest a iyakar Kaduna da Abuja.
Jami'an tsaron sun samu gagarumar nasara inda su ka cafke akalla miyagu hudu, da su ka hada da Yahaya Abubakar mazaunin Mpape, Mohammed Mohamed mazaunin Zuba, Umar Aliyu da Nura Abdullahi mazauna dutsen Zuba Kubwa.
A sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafinsu na facebook, rundunar ta bayyana cewa wasu bayanan sirri ne su ka taimaka mata wajen kai samamen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Channels Television ta tatattaro cewa jami'an tsaro sun tarwatsa sansanin 'yan ta'addan da su ka addabi al'umar birnin tarayya da kewaye.
Wadanda aka kama sun bayyana cewa su 'yan kungiyar ta'addancin da ake kira ‘Mai One Million’ ne, kuma sun dade su na satar mutane a Abuja.
Kakakin rundunar 'yan sandan 'yan sandan, SP Josephine Adeh ta tabbatar da ceto wasu da jama'a da miyagun su ka yi garkuwa da su, kuma an sada su da iyalansu.
Rundunar ta jaddada aniyarta na rubanya kokari domin tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
A wani labarin kuma kun ji cewa 'yan ta'adda sun kai mummunan hari karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba inda su ka yi barna matuka,
Mutane kimanin 11 'yan ta'addan su ka kashe a harin, yayin da mutane da dama su ka samu raunuka lokacin da su ke kokarin tsira da rayukansu.
Asali: Legit.ng