Home Back

Ana zaɓen majalisar dokoki a Faransa

bbc.com 2024/7/7
Masu zaɓe

Asalin hoton, AFP

A ranar Lahadin nan ne za a yi zagayen farko na zaɓen majalisar dokokin Faransa, inda ake sa ran jamiyyar masu tsattsauran ra'ayin riƙau ta National Rally za ta yi nasarar zama ta daya.

Za dai a yi zagaye na biyu na zaɓen mako ɗaya bayan na farko.

A zaɓen na zagayen farko masu tsananin ra’ayin riƙau suna kusa da kama mulki fiye da duk wani lokaci a zamanin nan a ƙasar ta Faransa.

Jam’iyyar ta National Rally (RN) ta Marine Le Pen da Jordan Bardella na kan gaba sosai a ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a – mako uku kafin ranar zaɓen, tun bayan da suka yi nasara a zaɓen majalisr dokokin Tarayyar Turai, abin da ya sa Shugaba Emmanuel Macron, ya mayar da martani ta hanyar kiran a yi zaben wuri, abin da ya wasu ke gani ya yi kasada.

Sama da mutum miliyan 2.6 daga cikin masu zabe na kasar miliyan 49 ne suka yi rijista don su yi zaben ta hnnun wasu ko wasu su kada kuriar a madadinsu.

Abin da ke nuna alamu na cewa za a fito sosai domin kada kuri’ar, tare da nuna muhimmancin zaben.

Zabe ne dai na zagaye biyu wanda kuma yawancin kujerun majalisar dokokin 577, sai a zagaye na biyu na zaben wanda za a yi mako daya bayan na yau, wato Lahadi mai zuwa za a yi zabensu.

An yi yakin neman zabe ne na kwana 20 kawai, kuma dadin dadawa wannan ya kara bai wa jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayin rikau ta RN wata dama, inda ta hakan ta kara jaddada alkawuranta kan batun baki da shige da fice da tsaro da rage haraji domin rage tsananin tsadar rayuwa a kasar ta Faransa.

Jordan Bardella na son zama Firaminista na farko na jam’iyyar ta RN, kuma jam’iyyar tasa na da kwarin gwiwar cin gomman mazabu tun a zagaye na farko na zaben.

To amma kuma ya ce ba zai karbi wannan mukami ba idan jamiyyar tasa ta samu gagarumar nasara ta kai tsaye ta kujeru 289.

Da zarar sakamakon farko ya bayyana a zaben na yau Lahadi , abokan hamayyar jamiyyar ta National Rally, dole su yanke shawara kan wanda za su mara wa baya a mazabun da za su kasance na raba-gardama a fadin kasar, domin dai su tabbatar da ganin ba ta samu gagarumin rinjayen na kai tsaye ba.

Idan har sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a ya kasance daidai to jam'iyyar ta National Rally za ta fafata ne da hadakar masu tsattsauran ra'ayin kawo sauyi, hadakar da aka yi cikin gaggawa wadda ake kira New Popular Front.

Ana sa ran hadakar Shugaba Macron ta samu kujeru baina-baina abin da ya sa ake ganin kwanakin Firaminista Gabriel Attal sun kawo karshe, duk da cewa kuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuna cewa shi ne har yanzu ya fi farin jini.

People are also reading