Home Back

Mutane 11 Sun Rasu, 30 Sun Jikkata A Rikicin Kabilanci A Filato – Gwamnati

leadership.ng 2024/5/12
Mutane 11 Sun Rasu, 30 Sun Jikkata A Rikicin Kabilanci A Filato – Gwamnati

Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane shida tare da jikkata 30 a rikicin kabilanci da ya barke a Karamar Hukumar Mikang ta jihar.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa, Mista Musa Ashoms ne, ya zanta da manema labarai a ranar Litinin a Jos.

Ya ce rikicin ya faru ne a ranar Lahadi a kauyukan Funyalang da Ponglong.

Ashom ya shawarci jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.

“Mun tashi jiya da labari marar dadi cewar mutane sun dauki makamai sun farmaki juna.

“Abin takaici, mutane shida sun rasa rayukansu kuma mutane kusan 30 da sun samu munanan raunuka, yayin da aka kone gidaje kusan 40 tare da kone rumbunan abinci.

“Abin da ya faru abun takaici ne.

“Al’amari ne da za a iya warware shi cikin ruwan sanyi, a cewar shugaban Karamar Hukumar Mikang.

Kazalika, Ashoms ya ce akwai kauyuka kusan 11 da su ma suka shiga fadan wanda ya kara dagula al’amura a yankin.

Sai dai ya yaba wa jami’an tsaro kan yadda suka kai samame yankin domin tabbatar da doka da oda.

Kwamishinan, ya ce al’amura sun daidaita a yankin, yayin da zaman lafiya ya samu.

“A matsayinmu na gwamnati, muna so mu fada wa mutane cewa ba za mu bari mutane su dauki makami su kashe junansu ba.

“Kamar yadda muka sha fada kullum, wannan ba abin da ya dace ba ne. Wannan Jihar Filato ce, karkashin jagorancin mai girma Gwamna Caleb Muftwang.

“Ba za mu kyale mutane su raba hankalinmu ba. Abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne ci gaban Filato,” in ji shi.

People are also reading