Home Back

Irin Sake Fasalin Kasar Da ‘Yan Nijeriya Ke So

leadership.ng 3 days ago
Irin Sake Fasalin Kasar Da ‘Yan Nijeriya Ke So

Cikin sabon salo, guguwar yekuwar neman ‘canji’ tana kadawa a duk fadin Nijeriya, har da ta hanyar da ba ta dace ba. Akwai kiraye-kirayen a sake fasalin harkokin siyasa da tattalin arziki, kai ka ce wannan shi ne babban batun da a halin yanzu yake damun ’yan Nijeriya wadanda suke kaka-ni-ka-yi a cikin annobar rashin samar da muhimman abubuwan da ke da muhimmanci a rayuwarsu da kuma gwagwarmayar wanzuwar rayuwarsu ita kanta.

‘Yan Nijeriya a gida da waje, sun yi ittifaki a kan cewa tabbas akwai abubuwan da ake yi ba daidai ba a tsarin siyasa, wanda dole ne a magance su idan har ba a so sauran kasashen duniya su tafi su bar mu a baya, kasancewar kusan tuni suka yi watsi da kasar nan wadda ta taba rike kambun zama zuciyar Afirka da take da mafi girman tattalin arziki a ma’aunin GDP.

Sun kuma yarda cewa zaren da ke rike da al’umma ya yi rauni sosai, ta yadda ya zama wajibi a yi taka-tsan-tsan don kar ya kara jin jiki fiye da halin da yake ciki a yanzu. Wannan ya haifar da tsattsauran ra’ayi na neman mafita ga kalubalen da ake fuskanta, kamar yadda masu goyon bayan sake fasalin suke yekuwa, inda hakan na iya zama cutarwa daga bisani, a kokarin gina kasar da masu kishin kasa suke fatan gani.

Yana da kyau a jaddada cewa, a wannan lokaci, kasar nan na bukatar jajirtattun maza da mata masu kishin kasa wadanda za su nuna da gaske suke yi wajen samar da kasa mai albarka da za a yi alfahari da ita. A halin yanzu, abin da ke mamaye sararin samaniyar kasar bai wuce hayaniya da yekuwar ‘yan ci-da -ceto da kuma ‘yan kwangilar siyasa ba masu neman cimma bukatun kawunansu. An siyasantar da lamarin ta yadda har ya rasa kima da mutunci a batun neman mafita ga kasa tare da daukar salon tafiyar hawainiya.

Tun bayan dawo da mulkin farar hula a shekarar 1999, wata da’irar siyasa ta sake fasalin tsarin mulkin Nijeriya inda ta ci gaba da dagewa wajen neman abin da ta dauka a matsayin maganin kalubalen da ke fuskantar al’ummar kasar nan. Wannan da’irar ta fara ce a farkon jamhuriya ta biyu inda ta kasance wani bangare ne na shafa mai a baki da yakin neman zabe. Dangane da haka, gwamnatin Obasanjo, a shekarar 2005, ta kira wani babban taron gyara harkokin siyasa na kasa. A shekarar 2014, Shugaba Goodluck Jonathan ya bi bayan taron inda ya sake shirya taron kasa, duk da cewa ba a dauki mataki kan sakamakon taron da aka yi kafin wannan din ba. Rahotannin tarukan guda biyu, yanzu haka suna can an jibge a dakunan karatu da wuraren ajiye kayan tarihi domin amfanin tsirarrun masana tarihi da masu bincike.

Daga irin wannan al’amari da yake faruwa, mu, a matsayinmu na jarida, mun fara nazarin sabbin kiraye-kirayen fara aiwatar da wani tsari wanda zai yiwu ya karkare a batun sake fasalin tsarin mulki. Wannan ‘canji’ ya sa aka yi gaggawar komawa tsohon taken kasa. Tuni dai dama, akwai yunkuri a Majalisar Dokokin Kasa game da yin watsi da tsarin shugabanci na shugaban kasa mai cikakken iko kwallin-kwal da nuna goyon baya ga koma wa tsohon tsarin amfani da majalisa da aka gada daga mulkin mallaka na Burtaniya a lokacin da muka samu ‘yancin kai. Hakazalika, wata kungiya a majalisar dokokin kasa na jagorantar wani yunkuri na sauya wa’adin shugabancin kasa ya koma tsawon shekaru shida sau daya tare da nada mataimakan shugaban kasa guda biyu da sauran rakiyar wasu bukatu da har yanzu ba a fayyace su ba. Mun damu kan cewa da irin wannan ne aka fara gangamin aikin neman wa’adi na uku na Obasanjo. Shin tarihi ya kusa maimaita kansa ne kuma su waye suka ci gajiyar abin?

Akwai kuma kiraye-kirayen a yi watsi da kundin tsarin mulkin 1999 na yanzu, wanda aka yi imanin cewa tarihi ne na mulkin kama-karya da shekarun da sojoji suka yi suna mulki, tare da ba da shawarar mayar da al’umma zuwa amfani da kundin tsarin mulkin 1963, wanda ya gaza kuma ya kusan kai ga wargajewar kasar. A ra’ayinmu, wannan na iya zai zama daidai da wani karin magana na turanci da ke cewa “zubar da ruwan wanka tare da jaririn da ake wankewa”. Dole ne a yi nuni da cewa sake fasalin kasar wani lamari ne da ya shafi tsarin mulki, mai sarkakiya wanda kuma bisa doka ba za a iya tafiyar da shi ba yadda ya kamata, a ganinmu, sai ta hannun Majalisar Dokoki ta Kasa mai kishin kasa na tsakani da Allah ba wadda take biyayya ga mai ba ta kudi ba ko kuma tunanin cin gajiyar abin daga bisani.

Muna goyon bayan samar da sabon kundin tsarin mulkin da za mu iya tabbatar da cewa ‘Mu al’ummar Nijeriya’ mun taka muhimmiyar rawa wajen samar da shi. Daga wannan hangen nesa kuma, muna ganin shawarar da ake ci gaba da yi ta mayar da Nijeriya tsarin ‘yan majalisa na zaben firaminista daga cikinsu, musamman amfani da kundin tsarin mulki na 1963, a matsayin abin da ya ginu a tsarin da ba za a amince da shi ba.

A namu ra’ayin, abin da ke da ban tsoro game da wannan sabon kira shi ne barazanar da ke tattare da yiwuwar wargajewar Nijeriya, fatan da ya kasance a zukatan wasu kasashen ketare saboda fargabar da suke da ita ta yiwuwar bunkasa da gyaruwar Nijeriya ta fuskar siyasa da tattalin arziki.

Bugu da kari a kan wannan, a ra’ayinmu, shin wannan ne ya haifar da matsalar kiraye-kirayen komawa ga tsarin shugabanci na yanki kamar yadda aka samu a jamhuriya ta farko? Shin babu wata matsaya da za a iya cimmawa a kan lamarin? Ai kirkiro da jihohi ya bai wa kabilun da ake ganin ana musu danniya damar amayar da abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. A wurinsu, komawa tsarin shugabanci na yanki ba komai ba ne illa tarihin da ba a bukatarsa. Tsarin Tarayya mai daidaito tare kyakkyawan tsarin siyasa ne suke fatan gani.

Dole ne a san cewa tsarin amfani da Majalisar Dokokin Nijeriya da ya yi aiki daga 1947 zuwa 1966 an gina shi ne bisa kurakuran da kundin tsarin mulkin baturen mulkin mallaka Richard ya shimfida. Shi ne kundin tsarin mulkin Nijeriya mafi rashin dacewa da dimokuradiyya da aka taba samu. Matsalarta ba ta yadda aka samar da kundin ba ne kawai; asalin ka’idojin da aka yi amfani da su, su ne ginshikin karkacewar siyasar Nijeriya har zuwa yau. Da gangan Turawan Ingila suka kirkiri ra’ayoyin yanki da suka saba wa asalin tsarin Nijeriya don cutar da muradunmu na ci gaban kasa baki daya.

A ra’ayinmu, duk wadannan batutuwa masu kawo rarrabuwan kawuna ne. Sun sha bamban da abubuwan da ‘yan Nijeriya ke tsammani musamman wajen fuskantar barazana ta kowane bangare kama daga rashin tsaron rayuka da dukiyoyi, matsalar abinci, rashin aikin yi, tsadar samun nagartaccen kiwon lafiya, matsalar makamashi, rashin saukaka hanyoyin kasuwanci har zuwa kan tabarbarewar abubuwan more rayuwa.

‘Yan Nijeriya na son tsarin da zai magance wadannan kalubalen na tattalin arziki da zamantakewa cikin gaggawa tare da ba su hujjar shiga dumu-dumu a dama da su cikin tsarin sake gina kasar. A nan kuma, ba dogon turanci ake bukata ba, aiki kawai!

People are also reading