Bola Tinubu Ya Tura Tallafi Ga Gwamna Abba Yayin da Ake Fama da Rikicin Sarautar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da gudunmawar kayan masarufi da yawansu ya kai tan 2,706 ga gwamnatin jihar Kano.
Shugaban ya abayar da waɗannan tulin kayan abinci ne domin rabawa mutane masu ƙaramin ƙarfi a faɗin kananan hukumomi 44 na jihar.
Daily Trust ta ce Tinubu ya miƙa tallafin da suka hada da masara, gero, dawa da garri ga gwamnatin Kano ta hannun hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da take miƙa kayayyakin a madadin Tinubu, Darakta-Janar ta hukumar NEMA, Zubaida Umar, ta jaddada kudirin shugaban kasa na rage raɗaɗin tsadar rayuwa.
A wannan kason, jihar Kano ta samu tan 969 na masara, tan 1,320 na dawa da tan 417 na gero, wanda ake sa ran za a rabawa maɓukata a faɗin jihar.
A wannam karon an ware kashi 20% ga ƙungiyoyin addinai yayin da kaso 3% za a rabawa makarantun kwana.
Zubaida Umar ta yi gargadi game da ambaliyar da aka yi hasashen zata iya faruwa a 2024 duba da hasashen yanayin da aka fitar na shekara-shekara.
Bayan karbar kayan, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin bin umarnin gwamnatin tarayya wajen raba kayayyakin.
Gwamna Abba ya yi kakkausar gargadi ga duk wani mai niyyar karkatarwa ko aikata munanan ayyuka a lokacin rabon kayayyakin.
Yayin da ya ke nuna jin dadinsa da karamcin shugaban ƙasar, gwamna ya bukaci ya ci gaba da tallafa wa al’ummar jihar Kano.
A wani rahoton kun ji cewa yayin da ake ci gaba da rigimar sarauta, kotu ta shirya yanke hukunci kan sabuwar dokar masarautar Kano.
Mai Shari'a Liman na babbar kotun tarayya ya sa ranar 20 ga watan Yuni domin yanke hukunci kan halascin mayar da Sarki Sanusi II.
Asali: Legit.ng