Home Back

Shugabannin Nijar da Mali da Burkina Faso na taro

dw.com 2024/10/5
Shugaban majalisar mulkin soji na Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani
Shugaban majalisar mulkin soji na Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani

A karon farko, kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da suke kwace mulki da tsinin bindiga daga hannun farar hula na gudanar da taro.

Shugabannin sun kafa kungiyar kawancen yankin Sahel wato AES  bayan fice wa daga ECOWAS  sakamakon dakatar da su daga harkokin kungiyar. Dama dai kasashen sun yanke alaka da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa, inda suka dasawa da Rasha.

Fadar shugaban kasa ta Burkina Faso ta ce, batun yaki da ta'addanci da kuma karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen su ne batutuwan da za su mamaye zauren tattaunawarsu. Kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sha fama da matsalolin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a kan iyakarsu wanda ya yi sanadin rayukan dakarun soji da kuma fararen hula da dama.

A gefe guda, shugabannin kungiyar ECOWAS za su gudanar da taron koli a Najeriya a ranar Lahadi.

People are also reading