Home Back

Majalisar Dokokin Jihar Imo Ta Dakatar da Mambobi 4, Ta Yi Garambawul

legit.ng 2 days ago
  • Shugaban majalisar dokokin jihar Imo, HonChike Olemgbe, a ranar Talata ya dakatar da ƴan majalisa huɗu bisa zargin kulla maƙircin tsige shi
  • Ya ce majalisar ta ɗauki wannan matakin ne a zaman sirri kuma daga yanzun an kwace dukkan kwamitocin da ke hannun ƴan majlaisar da aka dakatar
  • Sai dai har kawo yanzu babu wani martani daga ƴan majalisar da matakin ya shafa duk da wasu daga cikin sun halarci zaman yau Talata, 2 ga watan Yuli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Majalisar dokokin jihar Imo ta dakatar da ƴan majalisa huɗu bisa zargin suna yunƙurin tsige shugaban majallisar, Chike Olemgbe.

Kakakin majalisar Honorabul Olemgbe ne ya sanar da ɗaukar wannan matakin a zaman ranar Talata, 2 ga watan Yuli, 2024.

Majalisar dokokin jihar Imo.
Shugaban majalisar Imo ya dakatar da waɗanda ake zargin suka shirin tsige shi Hoto: Imo State House Of Assembly Asali: Facebook

‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da mamba mai.wakiltar mazaɓar Ahiazu-Mbaise, Samuel Otuibe da mai wakiltar mazaɓar Ezinihitte-Mbaise, Henry Agbasonu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sune mai wakiltar mazaɓar Okigwe, Chidiebere Ogbunikpa da takwaransa na mazaɓar Oru ta Yamma, Dominic Ezerioha

Shugaban majalisar ya ce an dauki matakin dakatar da su ne a zaman da mambobin majalisar suka yi cikin sirri ranar Talata.

Chike Olemgbe ya ƙara da cewa majalisar ta kuma kwace dukkan kwamitocin da ke hannun mambobin da aka dakatar.

Rahotanni sun bayyana cewa kakakin majalisar ya yi wasu ƴan gyare-gyare a kwamitoci a lokacin wannan zama da aka dakatar da ƴan majalisa huɗu.

Wasu daga cikin mambobin majalisar da aka dakatar waɗanda suka halarci zaman ranar Talata ba su yarda sun yi magana da ƴan jarida ba, cewar rahoton The New Telegraph.

A wani rahoton kun ji cewa

Asali: Legit.ng

People are also reading