Majalisar Dokokin Jihar Imo Ta Dakatar da Mambobi 4, Ta Yi Garambawul
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Majalisar dokokin jihar Imo ta dakatar da ƴan majalisa huɗu bisa zargin suna yunƙurin tsige shugaban majallisar, Chike Olemgbe.
Kakakin majalisar Honorabul Olemgbe ne ya sanar da ɗaukar wannan matakin a zaman ranar Talata, 2 ga watan Yuli, 2024.
‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da mamba mai.wakiltar mazaɓar Ahiazu-Mbaise, Samuel Otuibe da mai wakiltar mazaɓar Ezinihitte-Mbaise, Henry Agbasonu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sune mai wakiltar mazaɓar Okigwe, Chidiebere Ogbunikpa da takwaransa na mazaɓar Oru ta Yamma, Dominic Ezerioha
Shugaban majalisar ya ce an dauki matakin dakatar da su ne a zaman da mambobin majalisar suka yi cikin sirri ranar Talata.
Chike Olemgbe ya ƙara da cewa majalisar ta kuma kwace dukkan kwamitocin da ke hannun mambobin da aka dakatar.
Rahotanni sun bayyana cewa kakakin majalisar ya yi wasu ƴan gyare-gyare a kwamitoci a lokacin wannan zama da aka dakatar da ƴan majalisa huɗu.
Wasu daga cikin mambobin majalisar da aka dakatar waɗanda suka halarci zaman ranar Talata ba su yarda sun yi magana da ƴan jarida ba, cewar rahoton The New Telegraph.
A wani rahoton kun ji cewa
Asali: Legit.ng