Home Back

Magidanci zai yi zaman kurkuku na tsawon shekaru 17 bisa laifin yi wa ‘yarsa fyade da ɗirka mata ciki

premiumtimesng.com 2 days ago
Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

Kotu dake Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa ta yanke wa wani mahaifi mai shekara 41 Baridapsi Needem hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru 17 bayan an kama shi da laifin yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru 14 fyade da yi mata ciki.

Yarinyar ta haifi ‘ya mace kafin kotu ta yanke wa mahaifin hukunci.

Kungiya mai zaman kanta ‘Gender Response Initiative Team’ ta ce ta samu labarin abin da Needem ke aikatawa da ‘yarsa daga wajen wata makwabciyar su inda a lokacin yarinyar na da cikin wata biyar.

Kungiyar ta ce makwabciyar ta ce Needem ya rabu da matarsa wato mahaifiyar ƴarsa da tun bayan rabuwarsu ya maida ita matarsa.

“Mahaifin ya fara yi wa ‘yarsa fyade a shekarar 2020 inda a lokacin yatsun sa ne yake sakawa a gaban yarinyar sannan a 2022 ya rika danne ta har sai da ya ɗirka mata ciki.

A kotun lauyan da ya shigar da karar Pere Egbuson ya ce Needem ya fara yi wa ‘yar sa fyade tun tana shekara 7.

Egbuson ya gabatar da sakamakon gwajin DNA wanda ya tabbatar cewa Needem shine mahaifin jaririyar da ƴarsa ta haifa.

Alkalin kotun D.E. Adokeme ta yanke wa Needem hukuncin zama a kurkuku na shekara 17.

People are also reading