Home Back

Kasar Sin Ta Ba Da Shawarwari 6 Game Da Matakan Tsaro Yayin Tattaunawar Shangri-La

leadership.ng 2024/6/26
Kasar Sin Ta Ba Da Shawarwari 6 Game Da Matakan Tsaro Yayin Tattaunawar Shangri-La

A yau Lahadi ne ministan tsaron kasar Sin Dong Jun, ya gabatar da muhimmin jawabi a gun taron tattaunawar Shangri-La karo na 21 da aka yi a kasar Singapore, inda ya mai da hankali kan ra’ayin kasar Sin dangane da tabbatar da tsaron duniya. 

Dong ya ce, a wannan gabar da duniya ke fuskantar sauye-sauye, yana da matukar muhimmanci a kafa wani sabon tsarin hadin gwiwar tsaron yanki, wanda zai tabbatar da daidaita damar tofa albarkacin baki ga kasashen duniya, da kaucewa fadace-fadacen kungiyanci, da samar da mu’amala ta gaske, da sada zumunci da gaskiya kuma cikin daidaito.

Bisa wannan dalili ne kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda shida, wadanda suka hada da kiyaye halaltacciyar moriyar tsaro ta dukkan kasashen duniya, da samar da daidaito da adalci a tsakanin kasa da kasa, da yin amfani da tsarin tsaron shiyya-shiyya yadda ya kamata, da inganta hadin gwiwar tsaro bisa gaskiya kuma a aikace, da kafa misali a hadin gwiwar tsaron teku, da kuma inganta tafiyar da harkoki a yankuna masu bukatar tsaro.

Game da batun Taiwan, Dong Jun ya bayyana cewa, rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin PLA a ko da yaushe ta kasance wani karfi wajen kare dinkuwar kasar Sin. PLA za ta dauki kwararan matakai don dakile neman ‘yancin kai na Taiwan da tabbatar da cewa irin wannan makircin ba zai yi nasara ba.

Dong Jun ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta yi kira da a hada kai don samar da zaman lafiya, kana tana adawa da kulla kebabben kawancen soja dauke da mummunar manufa. Ya ce, “kananan kawance” daban daban dake harin wasu kasashe ba za su iya tabbatar da zaman lafiya a yankin ba, sai dai su haifar da karin tashin hankali.

Ya kara da cewa, sojojin kasar Sin za su dauki karin matakai a bayyane, da yin aiki tare da sojojin dake kasashen yankin, wajen gina wani sabon nau’in hadin gwiwar tsaro dake nuna daidaito, da amincewa da juna, da hadin gwiwar samun nasara tare.

Dong Jun ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na kara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya bisa kyakkyawan nufi kan rikicin Ukraine, kuma ba ta taba bayar da makamai ga kowane bangare na rikicin Ukraine ba. (Yahaya)

People are also reading