Home Back

Muna kiran jama'a da su daina bai wa jami'anmu nagoro - FRSC

bbc.com 2024/7/5

Muna kiran jama'a da su daina bai wa jami'anmu nagoro - FRSC

Mintuna 7 da suka wuce

Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa wato Federal Road Safety Corp, FRSC, Shehu Muhammad ya ce burinsa shi ne ganin ya rage yawan faruwar haɗurra da ma hana daƙile faruwarsu.

Ya ƙara da cewa suna ƙoƙarin ganin an fito da wani tsari da zai taƙaice yawan haɗurran da ke faruwa a ƙasar.

"Yanzu za ka ga akwai na'ura da idan mota za ta yi karo to za ta yi birki da kanta. Idan kuma za ta kauce to motar za ta dawo kan hanya. To irin waɗannan na'urori ne idan ƙasarmu ta ci gaba ya kasance ana sa su a motoci. Sannan akwai na'ura ma wadda take hana motar wuce gudun sa'a."

Shehu Muhammad ya ƙara da lissafa wasu hanyoyi da aka fi yin haɗurra a Najeriya guda biyu da suka haɗa da titin Mokwa wadda take da nisa sannan ba ta da kyau da kuma hanyar Kaduna zuwa Kano sakamakon yadda hanyar ta yi kyau masu ababan hawa na gudun yada ƙanen wani.

Daga ƙarshe shugaban hukumar ta kiyaye haɗurra ya ce manyan matsalolin da suke fuskanta da ke yi musu tarnaƙi wajen kai ɗauki ga masu ababan hawan da suka yi haɗari.

"Matsalolin da muke fuskanta su ne yawancin haɗurran nan na faruwa ne da daddare sannan ba mu da isassun ma'aikata da kayan aikin kai ɗaukin da daddare".

People are also reading