Home Back

Man United za ta sayar da Greenwood ga Marseille

bbc.com 2024/10/6
Mason Greenwood

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na tattaunawa da Marseille, domin sayar da Mason Greenwood ga ƙungiyar da ke buga Ligue 1.

Mai shekara 22 ya yi wasannin aro a Getafe mai buga La Liga a kakar da ta wuce, wanda ya ci ƙwallo takwas a fafatawa 33.

An yi ta alakanta shi da komawa manyan ƙungiyoyin Turai da taka leda, ciki har da Lazio da Juventus, amma Marseille ce kan gaba wajen son sayen ɗan wasan.

Ranar 30 ga watan Janairun 2022, United ta dakatar da Greenwood kan zargin da ya hada da wani bidiyon wata karamar yarinya a kafar sada zumunta.

A lokacin an zarge shi da laifin fyaɗe da cin zarafi daga baya wata kotun majistare ta wanke shi da soso da sabulu.

A cikin watan Fabrairu Sir Jim Ratcliffe ya sanar cewar United za ta sanar da makomar Greenwood kan fara kakar bana.

Greenword ya halarci wajen atisayen United a Carrington ranar Litinin, inda ya tattauna da mahukunta kan ƙungiyar da za su sayar da shi.

Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha'awar son ɗaukar ɗan ƙwallon.

People are also reading