Home Back

An Sake Tafka Babban Rashi Bayan Mutuwar Jarumin Fina-finai a Najeriya

legit.ng 2024/5/5
  • Masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood ta sake tafka babban rashi bayan mutuwar wani shahararren jarumi
  • A yammacin jiya Talata 23 ga watan Afrilu ne aka sanar da mutuwar jarumi Zulu Adigwe wanda ya ta da hankula
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai shirya fina-finai a masana'antar, Stanley Nwoke a shafinsa a Instagram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - An sake tafka babban rashi bayan fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Zulu Adigwe ya riga mu gidan gaskiya.

An sanar da rasuwar marigayin a yammacin jiya Talata 23 ga watan Afrilun wannan shekara.

Fitaccen jarumin fina-finai ya kwanta dama a Najeriya
Jarumin fina-finan Nollywood, Zulu Adigwe ya rasu. Hoto: @zuluadigwe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shirya fina-finai a Nollywood, Stanley Nwoke shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Instagram.

Stanley ya bayyana cewa har zuwa lokacin sanar da mutuwar marigayin ba a gano musabbabin mutuwar tasa ba.

"Ina mai bakin cikin sanar da ku cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Zulu Adigwe ya rasu."
"Musabbabin mutuwar jarumin har yanzu ba a fayyace ba, Allah ya masa rahama."

Lokacin da ya ke kan kaifnsa, Adigwe ya yi shura a fina-finai kamar su 'Living in Bondage' da 'Breaking Free' da sauransu.

- Stanley Nwoke

Bayanai na biyo baya...

Asali: Legit.ng

People are also reading