Home Back

Dalilin da ya sa Najeriya za ta ciwo bashin Dala biliyan 2.25 daga Bankin Duniya

premiumtimesng.com 2024/5/6
HAJJI 2024: Yadda Gwamnatin Tarayya, Kano, Bauchi, Kogi, Kebbi, Osun suka tallafa wa maniyyata da cikon kuɗin Hajjin bana

Najeriya na zuba idon karɓar lamuni na Dala biliyan 2.25 daga Bankin Duniya, wanda kuɗin ruwan sa bai wuce kashi 1% bisa 100% ba.

“Bashi lamuni ne mai kama da tallafi, domin biyan kuɗin sai nan da shekaru 40, kuma fara biyan ma sai an shekara 10 tukunna,” cewar wani jami’i.

Ministan Harkokin Kuɗaɗe Wale Edun, ya ce Najeriya ta ci jarabawar cancantar karɓar lamunin Dala biliyan 2.25 daga Bankin Duniya.

Edun ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai, wadda Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe da Babban Bankin Najeriya (CBN) suka shirya ta haɗin-gwiwa.

Sun shirya ganawa da manema labarai ɗin lokacin da suke halartar taron Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), a birnin Washington, D.C, Amurka.

Idan aka karɓo bashin za a tsunduma kuɗaɗen wajen ayyukan bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, yayin da ake fama da wannan gaganiyar ƙalubalen tsadar rayuwa a faɗin Najeriya.

Bankin Duniya ya na bai wa ƙasashe lamuni wanda babu kuɗin ruwa ko kuma mai kuɗin ruwa wanda bai wuce kashi 1% bisa 100% ba, domin su farfaɗo ko bunƙasa tattalin arzikin su.

Minista Edun ya ce lamunin babu takurawa a cikin yarjejeniyar karɓar sa, domin sai nan da shekaru 40 za a biya shi. Kuma kashi 1% bisa 100 ne kacal kuɗin ruwan sa.

“Hukumar Daraktocin Bankin Duniya sun amince su ba Najeriya wannan bashi na Dala biliyan 2.25, wanda arha ce ba ɓagas kamar tuwon-sadaka. Kuɗin nan kusan kamar ma kyauta zan iya kiran su.”

Ya ce ba abin nuna damuwa ba ne don an ciwo wannan bashi, domin Shugaba Bola Tinubu na nan ya na ƙoƙarin ƙara yawan ɗanyen mai da ake haƙowa kullum a Najeriya, daga ganga miliyan 1.6 zuwa ganga miliyan 2 a kullum.

Ya ce ta haka ake sa ran Najeriya za ta ƙara samun kuɗaɗen shiga waɗanda za su taimaka mata wajen riƙa biyan basussukan da ke kan ta.

Ya ce kuma gwamnati na maida hankali wajen lalubo wasu ƙarin hanyoyin shigowar kuɗaɗe.

Edun ya ce nan da ‘yan shekaru masu zuwa kuma gwamnati za ta ƙara kuɗaɗen haraji daga da kashi 10% zuwa kashi 18%.

People are also reading