Home Back

APC shiyyar Arewa ta Tsakiya ta nemi a maida masu shugabancin jam’iyya

premiumtimesng.com 2024/5/2
Ban yi kira da a tsige ko Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC ba – Gwamna Alia

Gungun wata ƙungiyar mambobin APC na Arewa ta Tsakiya, sun nemi uwar jam’iyya ta ƙasa baki ɗaya ta maida masu haƙƙin su na shugabancin jam’iyya, a Arewa ta Tsakiya.

Sun yi wannan roƙon a wani taron manema labarai da suka kira, ranar Alhamis, a Abuja.

Shugaban ƙungiyar mai suna Sale Zazzaga be ya yi wa manema labarai jawabi a madadin ƙungiyar, inda ya ce yankin Arewa ta Tsakiya an maida shi koma-baya a shugabancin APC, duk kuwa da irin namijin ƙoƙarin da yankin ya yi a zaɓen 2023.

Zazzaga ya ce Arewa maso Yamma, yankin da Ganduje ya fito, ya mamaye manyan muƙamai, shi kuma yankin Arewa ta Tsakiya, an maida shi saniyar-ware.

Ya yi kira ga jam’iyyar APC ta yi wa Arewa ta Tsakiya adalci, bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa na siyasa a cikin jam’iyyar APC.

“Bayan saukar Abdullahi Adamu daga shugabancin jam’iyya, an yi ta kira cewa a bar shugabancin APC a hannun wani ɗan yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da Adamu ya fito.

“Sai dai babban abin takaici shi ne ba a yi hakan ba, sai aka ba Arewa maso Yamma.

“To Arewa maso Yamma ita kaɗai ta samu manyan muƙamai har gida uku”, inji Zaggaga.

Arewa ta Tsakiya ke da Ganduje matsayin shugaban APC na ƙasa, sai Kakakin Majalisar Tarayya, Tajuddeen Abbas, sai kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin.

Tsohon Mataimakin Shugaban APC na Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ne jagaba wajen neman a bai wa Arewa ta Tsakiya shugabancin APC.

Ganduje ya shiga tsomomuwa tun bayan da shugabannin APC a mazaɓar sa ta ayyana dakatar da shi.

Ita dai Babbar Kotun Kano ta jaddada halascin dakatarwar da APC ta yi wa Ganduje a mazaɓar sa.

An gargaɗi Ganduje ya daina duk wasu ayyukan da ke alaƙanta shi da shugabancin APC, har bayan makonni biyu kafin ta yanke hukunci.

Babbar Kotun Kano ta tabbatar da halascin dakatarwar da Shugabannin APC na Mazaɓar Ganduje suka yi wa Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje.

Yayin da ake yanke hukunci a ranar Laraba, Babbar Kotun Kano ta kuma gargaɗi Ganduje cewa ya daina kiran kan sa a matsayin mamba na APC, domin a yanzu shi dakatacce ne.

Mai Shari’a Usman Na’abba ne ya yanke wannan a ranar Talata, kamar yadda wani kwafen shari’ar ya nuna, wanda gidan Talabijin na AIT da kuma jaridar Daily Trust da wasu jaridu suka wallafa.

Wannan umarnin da aka ba Ganduje ya biyo bayan ƙarar da Lauyan Haladu Gwanjo da Laminu Sani, mai suna Ibrahim Sa’ad ya shigar.

Gwanjo da Sani dai Shugabannin Zartaswa ne na APC a Mazaɓar Ganduje da ke cikin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, a Jihar Kano.

Sun ce sun shigar da ƙarar ce a madadin sauran shugabannin jam’iyyar na Mazaɓar Ganduje baki ɗaya.

Gwanjo wanda ya ce shi ne Mashawarcin APC a fannin Shari’a, shi ne kwanaki biyu da suka gabata ya bayyana sanarwar dakatar da Ganduje daga APC a Mazaɓar Ganduje.

Babbar Kotun Kano ta ce kada Ganduje ya ƙara shugabantar gudanar da duk wasu al’amurran da suka shafi APC a matakin shugabancin sa na ƙasa.

Mazaɓar Ganduje ta dakatar da shi ne bisa zarge-zargen harƙallar kuɗaɗen da gwamnatin Kano ke zargin ya tafka.

People are also reading