Home Back

Buƙatar Ƙungiyar Ƙwadago Na Mafi Ƙarancin Albashi ₦494,000, A Duk Shekara Gwamnati Za Ta Kashe Naira Tiriliyan 9.5, Ba Zai Dore Ba – Minista

leadership.ng 2024/6/26
Yajin aiki

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce mafi ƙarancin albashi na ƙasa N494,000 da Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) ke nema, wanda ya kai jimillar naira tiriliyan 9.5 a duk shekara, na iya gurgunta tattalin arzikin ƙasa da kuma kawo cikas ga jin daɗin ‘yan Nijeriya sama da miliyan 200.

Idris ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja, yayin da yake mayar da martani ga barazanar da ƙungiyar ƙwadagon ta yi na tafiya yajin aiki idan har ba a biya musu buƙatunsu ba.

Ya ce tayin na N60,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi, wanda ya kai ƙarin kashi 100 na mafi ƙarancin albashin da ake biya na shekarar 2019, ya samu karɓuwa daga ƙungiyar masu zaman kansu, wacce mamba ce na kwamitin ɓangarori uku na tattaunawar.

“Sabon tsarin albashi mafi ƙaranci na Gwamnatin Tarayya ya kai kashi 100 a kan mafi ƙarancin albashin da ake biya na shekarar 2019. Amma Ƙungiyar Ƙwadago ta buƙaci N494,000, wanda zai ƙaru da kashi 1,547 a kan albashin da ake biya.

“Mafi ƙarancin albashi N494,000 na ƙasa da ma’aikata ke nema zai kai adadin naira tiriliyan 9.5 da Gwamnatin Tarayya za ta biya.

“Ya kamata ‘yan Nijeriya su fahimci cewa, duk da cewa Gwamnatin Tarayya na son a ba ma’aikatan Nijeriya isasshen albashi, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai ƙarfafa duk wani mataki da zai kai ga asara mai ɗimbin yawa na ayyuka ba, musamman a kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda ba za su iya biyan albashin da Ƙungiyar Ƙwadago ta nema ba,” inji shi.

Ministan ya ce duk da cewa Ƙungiyar Ƙwadago ta damu da albashin ma’aikata kusan miliyan 1.2, Gwamnatin Tarayya ta damu da jin daɗin ‘yan Nijeriya sama da miliyan 200 bisa la’akari da ƙa’idojinta na araha, ɗorewa, da kuma lafiyar tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.

Idris ya yi kira ga Ƙungiyar Ƙwadago da ta koma kan teburin tattaunawa tare da rungumar albashi mai ma’ana da gaskiya ga mambobinsu.

Ya ce saboda jajircewar da gwamnatin Tinubu ta yi wajen kyautata rayuwar ma’aikata, za a ci gaba da bayar da albashin ma’aikatan tarayya N35,000 har sai an ɓullo da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

People are also reading