Home Back

Babu Wata Maganar Yunwa, Minista Daga Kano Ta Fadi Dalilin Fasa Rumbun Abinci a Abuja, Ta Yi Gargadi

legit.ng 2024/4/29
  • Ministar Abuja, Hajiya Mariya Mahmoud ta yi Allah wadai da bata garin da suka kai hari rumbun abinci a Abuja
  • Ministar ta ce wannan ba maganar yunwa ba ce daman sun saba sata kuma za su dauki mummunan mataki kansu
  • Mariya ta bayyana haka ne yayin da kai ziyara Gwaga-Tasha domin sanin asarar da aka tafka bayan fashi da kwashe kayan abinci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Karamar Ministar Abuja, Mariya Mahmoud ta soki wadanda suka fasa rumbun abinci a birnin Tarayya Abuja.

Ministar ta ce babu wani yunwa tattare da abin da mutanen suka yi daman sun saba aikata laifuka da sata.

Ministar Abuja ta yi magana kan satar da aka yi a dimbin abinci
Dakta Mariya ta ce fasa rumbun abinci ba yunwa ba ce sata ne. Hoto: Nyesom Wike, Mariya Mahmoud. Asali: Twitter

Menene Mariya ke cewa kan satar abinci?

Mariya ta bayyana haka ne yayin da kai ziyara Gwaga-Tasha domin sanin asarar da aka tafka bayan fashi da aka yi tare da kwashe kayan abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karamar Ministar ta bayyana aika-aikar a matsayin abin takaici inda ta ce hatta rufin ma'ajiyar da sauran kayayyaki an sace, cewar Leadership.

Ta kuma ba da tabbacin cewa za su samar da ofishin 'yan sanda a dukkan inda ake ajiye abincin domin samar da tsaro, cewar TheCable.

Matakin da Ministar ta ce za su dauka

A cewarta:

"Muna nan ne saboda abin takaici da ya faru inda matasa suka balle ma'ajiyar abinci tare da sace komai da ke ciki har da katanga.
"Ba iya abinci aka sace ba hatta rufi da tagogi da kofofi da kuma ofisoshi an balle su.
"Wannan sata ne ba wai yunwa ba, idan mutum yunwa ya ke ji ai ba zai sace kayayyakin da ke wurin ba, za su fuskanci hukunci dai-dai abin da suka aikata."

Mariya ta ce sun raba abincin har sau biyu, su na shirin rabiya a karo na uku ne aka kawo farmaki ma'ajiyar tare da sace kayayyakin.

Bata gari sun kai farmaki rumbun abinci

Kun ji cewa wasu matasa sun kai farmaki ma'ajiyar abinci da ke birnin Abuja inda suka tafka barna.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin halin matsi da tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

 
People are also reading