Home Back

Akan matsin rayuwa ya kamata ƙungiyoyin ƙwagado ku yi yajin aiki saɓanin Albashi – Human Rights

dalafmkano.com 2024/7/1

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan dan Adam ta kasa da kasa wato International Human Rights Commission, ta ce akwai kamata ya yi yajin aikin kungiyoyin ƙwadago ya mayar da hankali wajen magance matsalar hauhawar farashi da nemawa ƴan ƙasa mafita kan halin matsin da ake ciki mai-makon batun karin Albashi.

Shugaban ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Dala FM, a yau Litinin, biyo bayan tsunduma yajin aikin da manyan ƙungiyoyin biyu suka yi da suka fara daga yau Litinin, kan batun mafi ƙanƙantar albashi da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarki.

A cewar sa, “kamata ya yi ƴan ƙwadagon su tashi tsaye wajen lalubo hanyoyin da farashin kayayyakin amfanin yau da kullum zai sauka, domin amfanuwar ƴan ƙasa tare da kawo ƙarshen yawan tafiya yajin aikin da kungiyoyin kwadagon ke yawan yi a faɗin Najeriya, “in ji Bakoji”.

Bakoji, ya kuma ƙara da cewar ƴan kwadago a Najeriya basu wuce kaso ɗaya bisa Dari ba, duk da neman ƙarin albashin ba laifi ba ne, amma dai neman mafita akan matsin rayuwa yafi.

Ƙungiyar ƙwadagon dai ta ƙasa NLC, da takwararta ta TUC, sun tsunduma yajin aikin na sai baba ta gani ne da suka fara daga yau Litinin, akan batun ƙarancin albashi, da kuma batun ƙarin kuɗin wutar lantarki.

People are also reading