Home Back

Jamus ta sassauta izinin aiki a kasar

dw.com 2024/7/3
Hoto: Gints Ivuskans/AFP

Tsarin na bukatar masu neman aikin su mallaki wani kati da aka yi wa lakabi da 'Chancenkarte. Hakan na nufin masu sha‘awar samun aiki a Jamus za su iya neman visa ba tare da mallakar aikin ba. Samun katin na Chancenkarte zai bai wa masu shi damar zuwa Jamus domin su jaraba neman aiki a cikin shekara daya.


Kwarewa a harshen Jamusanci ko Ingilishi da mallakar shaidar digiri ko shekaru biyu na kwarewa a fannin da mutum ke son samun aikin na daga cikin abubuwan da ake bukata kafin samun zuwa Jamus ta wannan hanya.


Wannan dai na cikin jerin matakai dabam-dabam da hukumomin Jamus suka dauka a baya-bayan nan domin tunkarar kalubalen rashin ma'aikata da kamfanonin kasar ke fuskanta.
 

People are also reading