Karo Na 2: Ramin Hako Ma’adanai Ya Rufta da Mutane a Neja, Jama’a Sun Rasu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Rahotanni suna kara nuni da cewa an sake samun ruftawar ramin hako ma'adanai a jihar Neja.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutane sama da 20 sun mutu a hatsarin ramin ma'adanai garin Galkago da ke jihar.
Jaridar Leadership ta ruwaito shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) yana karin haske kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa ramin ya rufta ne a kauyen Bazakwoi a yankin Adnun da ke jihar, rahoton jaridar the Guardian.
Har ila yau an ruwaito cewa a jiya Alhamis, 13 ga watan Yuni ne lamarin ya faru yayin da mutane ke tsaka da hakar ma'adinai a ramin.
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) Alhaji Abdullahi Baba-Arah ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Alhaji Abdullahi Baba-Arah ya kara da cewa hatsarin shi ne na biyu cikin kwanaki 10 da suka wuce a jihar.
Har ila yau, shugaban NSEMA na jihar ya tabbata cewa an samu mutane uku da ruftawar ramin ya yi sanadiyyar mutuwarsu.
Shugaban ya kuma kara da cewa al'ummar wurin sun yi kokarin ceto mutum daya da bai riga ya mutu ba.
Abdullahi Baba-Arah ya kuma tabbatar da cewa a halin yanzu ba wani mutum da ya makale a cikin ramin.
A wani rahoton, kun ji cewa rayukan mutum uku sun salwanta bayan wani ramin haƙar ma'adanai ya rufto kan ma'aikata a Zamfara.
Rahotanni sun yi nuni da cewa ramin wanda ya rufto a ƙaramar hukumar Anka ta jihar ya kuma yi sanadiyyar jikkata rayukan mutum 11.
Asali: Legit.ng