Home Back

Hajji 2024: Alhazai 5 Daga Jihar Kebbi Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Saudiyya

legit.ng 3 days ago
  • Hajiya Maryamu Suleman Mayalo daga karamar hukumar Maiyama a jihar Kebbi ta riga mu gidan gaskiya ranar Lahadi a ƙasar Saudi Arabia
  • Wannan rashi ya sa adadin alhazan jihar Kebbi da suka rasu a lokacin aikin hajjin bana na 2024 ya kai biyar
  • Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya yi ta'aziyyar rasuwar Hajiya Maryamu tare da addu'ar Allah ya jiƙanta ya sa ta a gidan Aljannar Firdausi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Jihar Kebbi ta kara rasa hajiya a ƙasa mai tsarki a lokacin da aka fara jigilar alhazan Najeriya zuwa gida bayan kammala aikin hajjin bana 2024.

Hajiya Maryamu Suleman Mayalo daga ƙaramar hukumar Maiyama a jihar Kebbi ta riga mu gidan gaskiya a ƙasar Saudiyya.

Alhaza a ƙasar Saudiyya.
Hajjn 2024: Jihar Kebbi ta rasa mahajjata 5 a ƙasar Saudiyya Hoto: Inside The Haramain Asali: Facebook

Ta rasu ne a ranar Lahadi a Asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makka bayan ta yi fama da doguwar jinya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rasuwar Hajiya Maryama ta sa adadin alhazan jihar Kebbi da suka rasu a lokacin aikin hajjin bana a ƙasa mai tsarki ya zama biyar.

Shugaban hukumar jin adadin alhazai ta jihar, Faruk Musa Inabo ya tabbatar da rasuwar Hajiya Maryama a wata sanarwa da ya fitar.

Gwamna Nasir ya yi ta'aziyya

Gwamnan jihar Kebbi, Dokta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya yi alhini tare da miƙa sakon ta'aziyya bisa rasuwar Hajiya Maryama.

Ya kuma yi addu'ar Allah SWT ya gafarta mata kuma ya sa ta a gidan Aljannatul Furdausi.

Haka nan kuma Gwamna Nasir Idris ya roƙi Allah ya bai wa iyalanta ƙarfin guiwar jure wannan rashi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wannan rashi da jihar Kebbi ta yi ya zo ne a daidai lokacin da aka fara jigilar dawo da alhazan Najeriya zuwa gida bayan kammala aikin hajjin bana 2024.

Mahajjacin Najeriya ya maida kuɗin tsintuwa

A wani rahoton kun ji cewa Wani mahajjacin Najeriya ya kara mayar da makudan kudi da ya samu a Makka ga hukumar kula da mahajjata ta kasa (NAHCON).

Hakan na zuwa ne bayan wani mahajjacin daga garin Limawa na jihar Jigawa ya mayar da kudin tsintuwa a makon da ya wuce.

Asali: Legit.ng

People are also reading