Kungiyoyin Kwadago Za Su Koma Yajin Aiki a Ranar Talata? an Bayyana Gaskiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta musanta cewa za ta koms yajin aikin da take yi kan mafi ƙarancin albashi a ranar Talata, 11 ga watan Yunin 2024.
Ƙungiyar ta ce rahotannin da ake yaɗawa kan batun komawa yajin aikin babu ƙamshin gaskiya a cikinsu.
A cewar ƙungiyar, an sauya ma'anar abin da mataimakin babban sakataren ƙungiyar NLC na ƙasa, Chris Onyeka, ya faɗi a hirar da aka yi da shi a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata hira ta wayar tarho da jaridar Tribune, Chris Onyeka, ya bayyana cewa ba a fahimci kalamansa da kyau ba.
"Bidiyon tattaunawar da na yi da masu gabatarwa a shirin tashar Channels tv yana nan domin tabbatar da cewa ɓan taɓa cewa ƴan ƙwadago na iya komawa yajin aiki a ranar Talata ba."
"Sun tambaye ni ko ƴan ƙwadago za su koma yajin aikin gama gari da suka tsagaita."
"Na gaya musu cewa tunda gwamnati da ƴan ƙwadago sun amince su kammala tattaunawa cikin mako ɗaya, kuma wannan mako ɗayan zai ƙare a ranar Talata, ƙungiyoyin ƙwadagon za su yi zama kan tattaunawar domin samar da matsayarsu."
"Wannan ita ce amsar da na ba su, na yi mamaki yadda labarai ke yawo cewa na ce za a koma yajin aiki a ranar Talata."
- Chris Onyeka
Har yanzu kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya ba su cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata ba.
Yayin da gwamnatin tarayya ta yi tayin za ta biya N62,000, ƴan ƙwadagon sun dage a kan sai an biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Asali: Legit.ng