Home Back

Sojoji Sun Tarwatsa 'Yan Ta'adda Suna Shirin Taron Kitsa Manakisa a Kaduna, an Kashe Miyagu

legit.ng 2024/7/1
  • Rundunar sojojin Najeriya na kara samun galaba a kan 'yan ta'adda inda suka tarwatsa wasu daga cikinsu suna tsaka da gudanar da taron ta'addanci a jihar Kaduna
  • Kwamishinan lamuran tsaro da harkokin cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da nasarar a sanarwar da ya fitar ranar Juma'a, inda ya ce ayyuka suna kyau
  • Mista Aruwan ya kara da cewa jami'an sojojin sun samu damar hallaka 'yan ta'addan, ciki har da shugabanninsu bayan bayan sirri sun shaida cewa an hango miyagun na shirin taro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna- Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana jin dadin yadda jami’an tsaron Najeriya ke fatattakar ‘yan ta’adda da ta’addanci daga jihar a kokarin tabbatar da zaman lafiya.

A luguden wuta na baya-bayan nan da jami’an tsaro suka kai yankin Bula da ke dab da dajin Yadi a Giwa, sojojin Operation Whirl Punch sun tarwatsa taron yan ta’adda.

Senator Uba Sani
Sojojin sun tarwatsa taron yan ta'adda a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa an kashe miyagu da dama a harin ciki har da wasu daga shugabanninsu suna tsaka da kokarin taron yadda za su hada manakisar addabar mutanen Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati na farin ciki da nasarar sojoji

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta na jin dadin rahotannin yadda jami’an tsaro ke galaba kan miyagu da suka hana mutanen jihar Kaduna sakat.

Kwamishinan lamuran tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya shaidawa manema labarai hakan ta cikin sanarwar da ya fitar, kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Ya ce bayanan da gwamnati ta samu na nuni da cewa ana samun nasarar ne bayan samun ingantattun bayanan sirri da ke taimakawa ayyukan jami’an tsaro.

Yadda sojoji suka hallaka 'yan ta'adda

Mista Aruwan ya kara da cewa jami’an tsaron sun afkawa ‘yan ta’addan bayan an hango su da mugayen makamai suna shirin gudanar da taro.

Kwamishinan ya roki al’umar Kaduna su ci gaba da tuntubar gwamnati da dukkanin bayanan da za su taimaka wajen dakile harkokin ta’addanci a Kaduna.

Jami'an Sojoji sun yi taro a Kano

A baya mun ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da taro a Najeriya domin tattaunawa da jama'a a wani yunkuri da inganta alaka.

A taron da aka gudanar domin fito da manufofin rundunar, rundunar sojojin ta nemi hadin kan 'yan jarida kan hanyoyin da suka dace wajen isar da sako ga yan kasa.

Asali: Legit.ng

People are also reading