Home Back

Faransa za ta agazawa Ukraine da daruruwan tankokin yaki

dw.com 2024/5/18
Hoto: Thibault Camus/AP Photo/picture alliance

Ministan harkokin tsaron Faransa Sébastien Lecornu, ya ce kasarsa za ta tallafawa Ukraine da daruruwan tankokin yaki don kare kanta daga mamayar da Rasha ke mata, a daidai lokacin da aka shiga shekaru ta 3 da fara yakin.

Mr Lecornu ya ce za a fara kai agajin motocin yakin ne a farkon shekara mai kamawa, tare da makamai masu linzami da ke kakkabo jiragen yaki na sama, da dai sauran makaman yaki.

Makaman da Faransar za ta aikewa Ukraine dai tsoffi ne da aka samar da su tun a shekarar 1979, a kokarin da take na kawar da tsoffi tare da kera sabbi, in ji ministan tsaron na Faransa Sébastien Lecornu.

People are also reading