Home Back

Yan Sanda Sun Cafke Miyagu Suna Shirin Karbar Kudin Fansa a Neja da Kaduna

legit.ng 2024/6/29
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta samu gagarumar nasara kan yan ta’addan da ke kokarin karbar kudin fansa yayin da ta yi ram da su, da wani barawon mota
  • Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan da ya tabbatar da nasarar ya bayyana cewa sun samu rahotannin sirri kan yadda yan ta’addar ke karbar kudin fansa
  • Ana zargin Sani Amadu dan shekara 17, da Sani Lawal mai shekara 20 da Aliyu Usman mai shekaru 22 mazauna Dadin Kowa a karamar hukumar Tafa a jihar Neja da laifin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar- Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta taki sa’ar damke kasungurman masu satar mutane guda biyar da wani da ake zargi da satar mota.

‘Yan sandan sun kuma gano mota kirar Toyota Land Cruiser daga wanda ake zargi bayan umarnin da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar na ragargaza masu satar mutane.

Police
An kama wadanda ake zargi da garkuwa da mutane a Kaduna Hoto: Nigerian Police Force Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard News ta wallafa cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan ta cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis ya tabbatar da lamarin.

Kaduna: An kama masu satar mutane

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana yadda ta samu nasarar cafke wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a suna tsaka da kokarin karbar kudin fansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan ya bayyana cewa jami’ansu da ke Maigana sun samu rahoton sirri ranar 15 Yuni, 2024 kan wadanda ake zargi.

Daga nan ne baturen ‘yan sandan yankin ya ja tawagar jami’ai da ‘yan bijilanti suka dunguma yankin da aka shaida masu tare da cafke matasan su biyar.

A cikin watan Yunin nan rundunar ta cafke masu garkuwa da mutane da dama , kamar yadda Daily Trust ta wallafa cewa an kama wasu 'yan ta'adda biyar.

Wadanda aka kama sun hada da Sani Amadu dan shekara 17, da Sani Lawal mai shekara 20 da Aliyu Usman mai shekaru 22 dukkaninsu mazauna Dadin Kowa a karamar hukumar Tafa a jihar Neja.

An kama wanda ake zargi da satar mota a yankin Manya a Ungwan Romi, jihar Kaduna, inda aka gano mota baka Toyota Land Cruiser Jeep, ta 2013 model mai lamba KTU 886 JD.

Kaduna: Miyagu sun hallaka mutane 6

A wani labarin kun ji cewa wasu gungun yan ta’adda sun kai hari karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna inda suka hallaka mutanen da ba su yi masu laifin komai ba.

A harin da miyagun su ka kai yankunan Bauda da Chibiya a gundumar Maro, sun kashe mutane shida kamar yadda shugaban karamar hukumar, Ibrahim Gajere ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

People are also reading