Home Back

InnalilLahi: An Shiga Ɗimuwa Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Fitaccen Basarake a Taraba

legit.ng 2024/5/3
  • An shiga wani irin yanayi bayan wasu 'yan bindiga sun hallaka babban basarake, Abdulmutalib Nuhu a jihar Taraba
  • Maharan sun kai farmakin ne a daren jiya Alhamis 18 ga watan Afrilu inda suka hallaka basaraken a cikin fadarsa
  • Dan uwan basaraken ya tabbatar da kai harin a kauyen Sansani da ke karamar hukumar Gasol a jihar inda ya ce sun harbi wani matashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin wani fitaccen basarake a jihar Taraba bayan kai mummunan farmaki.

Maharan sun bindige Abdulmutalib Nuhu da ke sarautar kauyen Sansani a karamar hukumar Gasol a jihar, cewar Leadership.

Yan bindiga sun yi ajalin babban basarake a Taraba
Wasu 'yan bindiga sun hallaka nasara a jihar Taraba. Hoto: Nigeria Police Force. Asali: Facebook

Yaushe aka kai harin a Taraba?

Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis 19 ga watan Afrilu a yankin awanni kadan kafin gudanar da kasaitaccen bikin gargajiya a karamar hukumar Ibbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindigan sun durfafi kauyen Sansani da misalin karfe tara na dare inda suka wuce kai tsaye fadar Sarkin tare da hallaka shi, cewar Politics Nigeria.

Yayan marigayin mai suna, Nuhu Sansani ya ce maharan sun kawo farmakin ne da dare inda suka hallaka basaraken tare da tafiya da wayoyinsa.

Yadda maharan suka hallaka basaraken

"Su iso kauyen da misalin karfe tara na dare inda suka wuce kai tsaye fadar suka hallaka shi tare da ɗauke wayoyinsa guda biyu."
"Yayin da suke ficewa daga kauyen, sun ci karo da wani akan babur inda suka harbe shi har ya karye a kafa sannan suka yi tafiyarsu."

- Nuhu Sansani

Mukaddashin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP James Lashen ya ce ya na kan hanyar zuwa ofishinsu ba shi da labarin harin 'yan bindigan.

"Ba ni da masaniya, ina kan hanyar zuwa ofis, idan na samu wani karin bayani zan sanar da ku."

- James Lashen

'Yan Mata sun mutu yayin hatsarin jirgi

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan mata uku sun rasa rayuwarsu yayin hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja.

Lamarin ya faru yayin da 'yan matan suka kife a cikin kogi a kan hanyarsu ta zuwa gaisuwar salla a karshen mako.

Wani mai sana'ar su, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun ceto wasu mata da direban amma sun tsamo gawarwakin matan uku.

Asali: Legit.ng

People are also reading