Home Back

Hanyoyin Samun Rahamar Allah, Tausayinsa, Jinkansa Da Safsafcinsa, Daga Imam Murtadha Gusau

premiumtimesng.com 2024/6/29
Eid Prayer
Eid Prayer

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu alaikum

‘Yan uwana al’ummar Najeriya masu girma, masu daraja, ku sani lallai babu shakka, ana cikin damuwa a kasar mu mai albarka, to amma da ikon Allah duk yadda abubuwa suka yi tsanani, to sauki yana zuwa. Kar mu yanke kauna daga rahamar Allah da tausayinsa da jinkansa.

Allah Subhanahu wa Ta’ala yana da wasu Sunaye na musamman, masu girma. Wadannan Sunaye kuwa sune, Ar-Rahman da Ar-Rahim. Wadannan Sunaye na Allah mai girma da daukaka, suna nuni da irin dimbin rahamar Allah da tausayinsa ga bayinsa. Kuma wadannan Sunaye na Allah masu girma suna da tushe guda daya ne, wanda yake tabbatar da cewa lallai hakika Allah shine wanda yafi komai da kowa tausayi, rahama da jinkai, kuma wanda ba za’a taba samun wanda rahamar sa ta kai ta Allah ba.

Bayin Allah masu girma, to yanzu menene bambanci tsakanin wadannan Sunaye na Allah guda biyu, wato Ar-Rahman da Ar-Rahim? Malaman addinin Musulunci sun ce, shi dai sunan Allah Ar-Rahman, yana nuni ne game da yalwa, da dimbin rahamar Allah da tausayinsa da jinkansa, wadanda suka game dukkanin halittunsa, hatta wadanda ba Musulmi ba suna iya samun wannan rahama ta Allah gamammiya. Shi yasa zaka ga da irin wannan rahama ta Allah, kai Musulmi kaji dadi ka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da arziki da walwala, idan kabi hanyar da Allah ya tsara abi domin a same su, haka shi ma wanda ba Musulmi ba, zai iya samun duk wadannan abubuwa da na lissafa, matukar yabi hanyar da ta dace ta neman su. Kai babu ruwan Allah, wanda ba Musulmi ba ma, yana iya fin ka jin dadi, kai Musulmi, matukar yabi hanyar da ta dace, kai kuma ka kwanta kaki nema ko kaki bin hanyar.

A daya gefen kuma, sunan Allah Ar-Rahim, shi kuma yana nuni da irin dimbin rahamar Allah, da falalarsa, da tausayinsa, da jinkansa na musamman, wadanda ba kowa yake samun su ba, sai bayinsa zababbu kawai; wannan ita ce rahamar Allah Subhanahu wa Ta’ala ta musamman, zuwa ga bayinsa muminai.

To yanzu irin wannan rahama ta Allah, da tausayinsa, da jinkansa, da falalarsa, musamman, irin wadda ya kebe ga bayinsa muminai, ta yaya zamu same ta, musamman a cikin irin wannan yanayi da muka samu kan mu a ciki, wanda muke neman rahamar Allah? Shin haka kawai ne ake samun irin wannan rahamar, ko kuwa dole, akwai hanyoyin da zamu bi domin samun ta?

To yanzu dai bari muyi nutso, muyi iyo cikin littafin Allah (Alkur’ani mai girma) da sunnar Manzonsa (SAW), domin lalubo amsar wannan bayani.

Hanyoyin da Al’ummah zata bi, ko zata koma gare su, matukar muna son Allah ya tausaya muna, sune a takaice kamar haka:

1. Yin da’a da biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW). Wannan yana saukar da rahamar Allah a bayan kasa. Domin Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:

“…kuma kuyi da’a ga Allah da Manzonsa sai ku samu rahamarsa.” [Surah ta 3:132]

2. Bin littafin Allah, Alkur’ani, sau da kafa. Yawan karanta shi da kuma aiki da abinda aka karanta. Shi ma babu shakka, tabbas, wannan yana jawo saukar rahamar Allah ga bayinsa.

Allah Madaukakin Sarki yace:

“Wannan shine littafi, wanda muka saukar mai albarka, don haka ku bi shi, kuma kuji tsoron Allah, domin samun rahamarsa da tausayinsa.” [Surah ta 6:155]

3. Mu zamo masu tsoron Allah. Tsoron Allah yana hana barna da ta’addanci a bayan kasa, sanadiyyar haka sai rahamar Allah ta sauka ga bayinsa. Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:

“Ya ku wadanda suka yi imani! Kuji tsoron Allah, kuma kuyi imani da Manzonsa, idan kuka yi haka, zai baku ninki har biyu na rahamarsa, sannan zai sanya maku wani haske wanda zaku yi tafiya da shi. Sannan ya gafarta zunuban ku. Kuma Allah mai yawan gafara ne, kuma mai jinkai.” [Surah ta 57:28]

Kuma Allah Ta’ala yace:

“Rahamata da tausayina sun yalwaci dukkan komai, kuma da sannu zan sanya su ga masu tsoron Allah.” [Surah ta 7:156]

4. Kyautatawa, tsakanin bawa da Allah mahaliccinsa, da kuma kyautatawa tsakanin bayin Allah.

Kyautatawa dukkanin halittun Allah yana saukar da rahamar Allah a bayan kasa. Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa:

“Hakika rahamar Allah tana kusa ga masu kyautatawa.” [Surah ta 7:156]

5. Yin Sallar nafilah raka’ah hudu, kafin sallar la’asar. Shi ma wannan lallai hanya ce babba, mai girma, ta samun rahamar Allah, da tausayinsa, da jinkansa.

Manzon Allah (SAW) yace:

“Ya Allah kayi rahama da jinkai ga duk wanda yake sallar nafilah raka’ah hudu kafin sallar la’asar.” [Tirmizi ne ya ruwaito shi, kuma yace Hadisi ne Hasan, haka ma Shaikh Muhammad Nasiruddin Al-Albani yace Hadisi ne Hasan, a cikin littafinsa, Sahihul Jami’]

6. Sauraron karatun Alkur’ani mai girma cikin da’a, ladabi da natsuwa. Yawan sauraron karatun Alkur’ani mai girma yana saukar da rahamar Allah.

Allah Ta’ala yace:

“Idan ana karanta Alkur’ani, ku saurare shi da natsuwa, domin samun rahamar Allah.” [Surah ta 7:204]

7. Tausayawa bayin Allah.

Imamu Ahmad ya fitar da Hadisi a cikin Musnad din sa, cewa Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Ku tausayawa bayin Allah, kuma sai Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tausaya maku. Ku yafewa bayin Allah, kuma sai Allah ya yafe maku.”

Kuma Hadisi ya tabbata cikin Sunan na Abi Dawud, cewa, Annabi (SAW) yace:

“Masu nuna tausayi da rahama da jinkai ga bayin Allah, su ma Allah mai rahama zai tausaya masu. Ku tausaya wa wadanda suke a bayan kasa, kuma sai Allah da yake sama ya tausaya maku.”

Don haka kenan idan muna son rahamar Allah, to sai mun nuna tausayi da rahama ga bayin Allah.

8. Umurni da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki a cikin al’ummah; kula da sallah da kiyaye ta a cikin lokacin ta; fitar da hakkin Allah daga cikin dukiyoyin mu, wato fitar da Zakkah. Wadannan duk hanyoyi ne na jawo rahamar Allah cikin al’ummah.

Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa:

“Muminai maza da mata, sun kasance majibinta juna ne; suna umurni da kyakkyawa kuma suna hani da mummuna; suna tsayar da sallah, suna bayar da zakkah, kuma suna yin da’a da biyayya ga Allah da Manzonsa. Allah zai saukar da rahamarsa zuwa ga re su. Hakika, Allah ya kasance mai karfi kuma mai hikima.” [Surah ta 9:71]

9. Sulhunta tsakanin mutane masu husuma ko masu fada ko masu wata hayaniya ko rashin jituwa ko adawa da juna. Lallai wannan wata babbar hanya ce da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya sanya wa bayinsa, domin suyi amfani da ita wurin magance matsalolinsu, domin amfana da juna, da samun zaman lafiya da yalwar arziki mai dorewa cikin al’ummah.

Allah Ta’ala yana cewa:

“Muminai ‘yan uwan juna ne. Don haka kuyi sulhu tsakanin ‘yan uwan ku, kuma kuji tsoron Allah, sai ku samu rahamarsa.” [Surah ta 49:10]

10. ‘Yan kasuwa da masu arziki su sanya tausayi, rahama da jinkai a cikin kasuwancin su.

Jabir Dan Abdullahi yace, Manzon Allah (SAW) yayi addu’a yace:

“Ya Allah, ka sanya rahama, tausayi da jinkai ga dan kasuwar da ya tausaya wurin saye da wurin sayarwa, da kuma wurin karbar kudin da yake bi bashi.” [Bukhari ne ya ruwaito shi]

Lallai yana daga cikin abubuwan da suke jefa wannan al’ummah cikin bala’i da rudu, da damuwa, akwai rashin tausayi da rashin imani a wurin wasu daga cikin ‘yan kasuwar mu da masu arzikin mu. Shi yasa Annabi Muhammad (SAW) yayi kyakkyawar addu’a, ga duk Dan kasuwar da ya sanya tausayi da imani a cikin kasuwancinsa.

A yau, an wayi gari, wasu daga cikin ‘yan kasuwar mu da masu arzikin mu wallahi sun lalace, sun zama ‘yan jari hujja, sun zama kamar yahudawa a cikin huldodin su. Basu da aiki sai shan jinin talakawa bayin Allah.

Zaka ga dan kasuwa, ko wani mai arziki, kawai wai don suna da kudi, za su sayi kayan abinci su boye, da nufin sai yayi tsada su sayar, suci kazamar riba. Kuma alhali suna sane da cewa, wallahi wannan haramun ne, haramun ne, haramun ne, Allah ya hana!

Kuma sun san wannan mugun hali nasu yana jefa al’ummah cikin tashin hankali da bala’i. Kawai su dai idan zasu samu kudi, to kowa ma ya mutu. Fa inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!

Kuma wai mai irin wannan halin, wai shi yana lissafa kan sa a cikin wannan al’ummah ta Annabi Muhammad (SAW).

Don Allah ta yaya Annabi zai yi alfahari da irin wadannan mutane masu jefa al’ummarsa cikin damuwa?

Tir da irin wannan hali nasu, kuma wal iyazu billah, muna neman tsarin Allah daga dukkanin wani mutum, da yake da hannu cikin jefa al’ummar Annabi (SAW) cikin damuwa.

Wannan mutum mai irin wannan mummunan hali, mai ci da gumin talakawa, makiyin Annabi ne, kuma makiyin al’ummar Annabi ne. Domin shi dai Annabi (SAW), wallahi alkhairi ya kawo wa duniya baki daya, don haka duk wani mabiyinsa, in dai har da gaske mabiyinsa ne na gaskiya, to tabbas, zaka same shi yana kokari wurin kawowa duniya alkhairi, ba sharri ba.

Kuma su irin wadannan ‘yan kasuwar da masu arzikin, su sani, duk abunda suke yi fa Allah yana sane, kuma yana kallon su. Kar suyi tsammanin wai don Allah ya bar su suna ta abunda suka ga dama, kamar bai san dasu ba ne, wallahi duk lokacin da Allah zai kama su zasu yi mamaki.

Allah ya ga damar sai sun gama tara dukiyar, sai ya sauko da wani bala’i, ko wata gobara ta lashe dukkan dukiyar. Ko kuma sai Allah ya kyale shi, sai ya tara dimbin dukiyar, sai Allah ya jarabe shi da wata irin rashin lafiya, ko wani ciwo, ko wata irin cuta ta musamman, duk ya lakume duniyar baki daya, kuma yaki warkewa. A tafi Amerika, a tafi Jamus, a tafi Faransa, a tafi Ingila, a tafi Indiya, kai ko’ina a tafi, amma a rasa lafiya, Allah ya rike lafiyar, ya hana a samu lafiyar, sai duk komai nasa ya kare, kuma ya mutu a wulakance.

Ko kuma ya gama tara dukiyar da gumin bayin Allah, ya mutu, ya bar wa iyalansa gado, su yi ta shaye-shaye da zinace-zinace da dukiyar, duk saboda alhakin bayin Allah.

11. Shugabanni da mabiya kowa yayi abunda ya dace, kuma kowa yayi abunda yake shine daidai daga bangarensa.

Shugabanni su tsara tsare-tsaren gwamnatocinsu (policies) a bisa tausayi da imani da kishin kasa da kyautatawa mabiya da rahama zuwa ga bayin Allah. Su kuma mabiya suyi wa Shugabanninsu addu’a kan Allah ya datar da su.

Mu sani, manufar ko wane shugabanci shine, samar wa da ‘yan kasa baki daya hanyoyin da zasu saukaka masu rayuwa, su samu su bauta wa Allah cikin walwala da zaman lafiya da yalwar arziki da annashuwa da son juna. Duk shugabancin da bai samar da wannan ba, to sai dai muce wallahi an samu akasi.

Mu sani, samun saukin al’ummah shine alamar shugabancin shugaba yayi kyau. Shiga tsananin da al’ummah zata yi kuwa, yana tabbatar da cewa shugabanci bai yi kyau ba. Allah ya sawwake, amin.

Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da idan muka daure muka bi su, to da izinin Allah, zamu samu rahamar Allah da tausayinsa da jinkansa da kuma safsafcinsa.

Amma matukar ba mu daure muka bi wannan hanya ba, to sai dai muce Allah ya sawwake, amin.

Ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tausaya muna, amin.

Ya ku bayin Allah! Kamar yadda kuka sani, yanzu muna fuskantar Ibadar Layyah, sallar idi, azumin Arfah da sauransu. Don haka daga cikin abubuwan da ake so game da Layyah sune kamar haka:

1. Ana yanka dabba ne bayan an kammala Sallar Idi, da kuma cikin kwanakin Ayyamut Tashrik, wato kwanaki uku bayan sallah.

2. Yanka lafiyayyar dabba, kuma ta kasance daga cikin dabbobi na ni’ima ne (wato Rago ko Tunkiya, Akuya ko Bunsuru, Rakumi ko Rakuma, Sa ko Saniya).

3. A Wasa kaifin wukar yanka, saboda kada dabba ta sha wahala wurin yanka.

4. Ambaton sunan Allah yayin yanka (Bismillahi, Allahu Akbar, Allahummah takabbal…); kuma a fuskanci Alkibla da dabbar.

5. Anfi so mai dabba ya yanka dabbarsa da kansa (wato da hannunsa).

6. Yana da kyau mutum yayi sadaka da naman (danye).

Daga cikin abubuwan da ya kamata mutum yayi lokacin sallar idi:

1. Kabarbari, za’a fara yin su ne tun lokacin fitowar Alfijir na ranar Arfah, har zuwa la’asar ta karshen Ayyamut Tashrik (kuma a bayyane za’ayi kabarbarin; a gidaje, da masallatai, da kasuwanni, da kuma bayan sallolin farillah da sauransu).

2. Yin wanka da sanya turare (amma ga maza kadai), da kuma sanya kaya mafi kyau cikin tufafin mutum.

3. An so mutum ya tafi zuwa masallacin idi da kafa (wato tattaki).

4. Kuma har kananan yara da mata zasu tafi idi, kai hatta mata masu jinin al’ada sukan tafi idi, sai dai ba za suyi sallah ba, zasu tsaya ne a gyefe suna kabarbari.

5. An so a canza hanyar tafiya da ta dawowa.

6. Gaisuwa ga ‘yan uwa musulmai, tare da ce masu:

“TAKABBALALLAHU MINNA WA MINKUM.”

7. Ana so a sada zumunci, da yin sadaka.

Daga karshe ina rokon Allah ya sanya Ikhlasi cikin Ibadun mu, kuma ya sanya mu cikin bayinsa wadanda zai karbi ibadun su, amin.

People are also reading